Home Back

‘Gwajin DNA ya nuna MKO Abiola ‘ya’ya 55 kaɗai ya haifa, ba 103 ba’, inji ɗan sa Abdulmumini

premiumtimesng.com 2024/7/3
MKO-Abiola
MKO-Abiola

Ɗaya daga cikin ‘ya’yan marigayi Cif MKO Abiola, wato Abdumumuni Abiola, ya bayyana cewa mahaifin su Mashood Kashimawo Olawale (MKO) Abiola, ‘ya’ya 55 ya haifa, kamar yadda gwajin DNA ya tabbatar, ba guda 103 kamar yadda ake ta yayatawa ba.

Abdulmumuni ya bayyana haka a cikin wata tattaunawar da aka yi da shi da Seun Okinbaloye, na Gidan Talbijin na Channels, wadda aka watsa a ‘YouTube’.

Ya ce kafin a yi gwajin DNA, mahaifin sa an yi ta iƙirarin cewa ya na da mata 40 da ‘ya’ya 103.

“Iyalan Abiola ba su da yawan da aka riƙa yayatawa. Ba mu da yawa, dududu mu 55 ne ya haifa. Matan sa kuma 40 ne. Ko kuma na ce 40 da ɗoriya, kamar yadda kwafen wasiyyar maciya gado ya tabbatar. Kuma ina jin yawancin matan na da ‘ya’yan da ba su wuce ɗaya ko biyu ba tare da baba na.

“Amma lokacin da mahaifi na ke raye, ya na biya wa yara 103 kuɗin makaranta. Amma kamar yadda na ce, ba dukkan su ba ne ‘ya’yan sa. Wasu ba ‘ya’yan sa ba ne. Mu ‘ya’yan sa 55 ne. Ka ga ba ma wani yawa gare mu ba kenan, bisa la’akari da idan ka kwatanta yawan ‘ya’ya miliyan 200 da Najeriya ke da su.

“Wato ina tunanin mahaifina ya ji daɗin rayuwar sa ne, amma ba ƙololuwar jin daɗi sosai ba. Dududu fa ‘ya’yan sa 55 duk da irin lokaci da sharaɗin da ya yi a duniya.”

Ya ce lokacin da gwajin DNA ya tabbatar da ‘ya’ya 55, ya tuntuɓi wasu da aka tabbatar ‘ya’yan na Abiola ɗin ne, lokacin su na ƙanana.

Ya ƙara da cewa, da suka kai munzilin balaga kuwa ya tuntuɓi dukkan su, domin a sake tsari da fasalin harkokin hada-hadar mahaifin na su, amma shirin bai yiwu ba.

Ya ce daga cikin wasiyyar da Abiola ya bari, shi ne cewa, “a sayar da dukkan kadarorin sa, bayan an bai wa matan sa na su kaso na gado. Sauran kadarorin da aka sayar kuma a raba kuɗin ga ‘ya’yan sa.”

Abdulmumin shi ne ɗan marigayiya Kudirat Abiola, wadda ita ma kashe ta aka yi a ranar 4 ga Yuni, 1996, a Legas.

People are also reading