Home Back

Fenerbahce ta gabatar da Mourinho a matakin sabon kociyanta

bbc.com 2024/7/8
Jose Mourinho

Asalin hoton, Getty Images

Fernerbahce ta gabatar da Jose Mourinho a matakin sabon kociyanta ranar Lahadi, wanda zai fara jan ragama daga kakar tamaula mai zuwa.

Ya maye gurbin Ismail Kartal, wanda ya bar kungiyar ranar Juma'a duk da wasa ɗaya kacal ya yi rashin nasara a kakar da ta kare da hada maki 99.

Wannan shi ne karon farko da ɗan kasar Portugal zai horar da ƙungiya tun bayan Roma da ta kore shi a Janairu, bayan kaka biyu da rabi a Italiya.

Dubban magoya bayan ƙungiyar ne suka yi wa Mourinho maraba a filin da ake kira Sukru Saracoglu.

To sai dai har yanzu ba a fayyace ƙunshin yarjejeniyar da aka kulla ba tsakanin ƙungiyar da kociyan.

Jose Mourinho

Asalin hoton, Getty Images

Jose Mourinho ya gabatar da jawabi gaban dubban magoya bayan da suka je yi masa maraba a matakin sabon kociyan Fenerbahce.

Ya ce: "Wasu lokutan ana ƙaunar koci bisa yawan nasarorin da ya samu. A wannan lokacin ina jin cewar ana ƙaunata a nan tun kafin nasarorin.

''Wannan wani babban nauyi nake jin an dora min. Na yi muku alkawari tun daga wannan lokacin ina daya daga cikin iyalanku. Wannan rigar kungiyar tamkar fatar jiki na ce.''

Mourinho ya horar da manyan ƙungiyoyi da yawa da suka hada da Chelsea da Real Madrid da Inter Milan da kuma Manchester United.

Shi ne kadai kociyan da yake da tarihin lashe Champions League da Europa League da kuma Europa Conference League.

Cikin shekara 24 da ya yi yana horar da tamaula a duniya, ya lashe manyan kofi 21.

Jose Mourinho

Asalin hoton, Getty Images

People are also reading