Home Back

Femi Otedola vs Jim Ovia: Manyan Attajirai 2 a Najeriya na Rigima Kan Almundahanar Kudade

legit.ng 2024/7/6
  • Femi Otedola ya zargi shugaban bankin Zenith da yi amfani da asusun kamfaninsa na bankin ba tare da izni ba
  • Hakan dai ya kawo rikici a tsakanin attajiran guda biyu waɗanda suke daga cikin attajiran da ake taƙama da su a ƙasar nan
  • Otedola dai ya yi zargin cewa an yi amfani da asusun na kamfaninsa da ke bankin ba tare da izninsa ba inda aka gudanar da harkokin kasuwanci da shi

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Legas - Rigima ta ɓarke tsakanin attajirin ɗan kasuwa, Femi Otedola da Jim Ovia, shugaban bankin Zenith.

Rikicin da ke tsakanin attajiran biyu dai ya samo asali ne kan zargin almundahanar kuɗi ta miliyoyin Naira.

Femi Otedola ya zargi Jim Ovia
Femi Otedola ya fallasa badakalar kudade a asusunsa na bankin Zenith Hoto: Bloomberg Asali: Getty Images

Wane zargi Femi Otedola ya yiwa Jim Ovia?

Femi Otedola ya zargi Jim Ovia da yin amfani da asusun kamfaninsa, 'Seaforce Shipping Limited' na bankin Zenith domin yin kasuwanci da shi ba tare da izninsa ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Duk da cewa ba a yi aiki da asusun ba tun shekarar 2010, an ci gaba da yin amfani da asusun na Seaforce ana harkokin kasuwanci ba tare da sanin Otedola ba, cewae rahoton jaridar TheCable

Otedola ya ce kamfanin Seaforce bai taɓa nema ko cin bashi daga bankin Zenith ba, amma an ci gaba da yin harkokin kasuwanci da asusun ba tare da izni ba.

Yaushe Otedola ya gano badaƙalar?

Otedola ya gano hakan ne cikin ƴan kwanakin nan, shekara 13 bayan an gudanar da harƙallar, bayan wani mai leƙen asiri a bankin Zenith ya sanar da shi.

Lokacin da ya ƙalubalanci jami'an bankin kan abin da ke faruwa, sai suka ba shi haƙuri.

Otedola ya samar da wata takarda wacce bankin Zenith ya rubuta a ranar 19 ga watan Maris, 2018 zuwa ga 'Shofolawe-Bakare & Co' masu binciken kuɗi na kamfanin Seaforce.

A cikin takardar sun bayyana cewa akwai bashin N2,278,420 a asusun maimakon N5bn da ke a jikin bayanan asusun bankin wanda jaridar TheCable ta gani.

Femi Otedola na son gano gaskiya

Otedola ya buƙaci sanin wanda ya biya kuɗaɗen domin rage bashin daga N16,927,628,581.84 zuwa N11,010,924,522.71 saboda bai san an yi hakan ba.

An saka N77,169,375.00 a ranar 18 ga watan Afrilu, 2011, N119,822,762.50 a ranar 01 ga watan Disamba, 2011, N316,537,329.30 a ranar 8 ga watan Disamba, 2011, N266,361,104 .50 a ranar 12 ga watan Disamba, 2011.

A sakamakon haka yanzu Seaforce yana da bashin N5,916,704,059.13 wanda mafi yawansa kuɗin ruwa ne.

Tuni ƴan sanda suka yiwa wani babban jami’in bankin tambayoyi.

Otedola zai bunƙasa ilmi

A wani labarin kuma, kun ji cewa Femi Otedola, Aliko Dangote, da Nyesom Wike za su gina ƙarin gidajen ma'aikata da ɗakunan kwanan ɗalibai a makarantun koyon aikin shari'a na Najeriya.

Darakta janar na makarantar, Farfesa Isa Hayatu, shi ne ya tabbatar da hakan inda ya yaba musu kan wannan kyakkyawar niyyar ta su. Read

Asali: Legit.ng

People are also reading