"Ba Za Ku Ci Banza Ba": An bukaci Gwamna Ya Binciki Ciyamomi Masu Barin Gado
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Rivers - Kungiya a jihar Rivers ta bukaci Gwamna Siminalayi Fubara ya binciki shugabannin kananan hukumomi masu barin gado.
Kungiyar Rivers Development Foundation (RiDeF) ta ce akwai zargin karkatar da kudi daga asusun Ζ™ananan hukumomi kan shugabannin.
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da kungiyar ta fitar a jiya Juma'a 7 ga watan Yuni, cewar TheCable.
Shugabar kungiyar, Rejoice Okoli ta bukaci Fubara ya kafa kwamitin bincike domin bankado badakalar ciyamomin.
"Kungiyar RiDeF tana kira ga Gwamna Siminalayi Fubara kan zargin badakala a shugabancin kananan hukumomi."
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Akwai manyan zarge-zarge kan shugabannin kananan hukumomin jihar masu jiran gado."
"Muna rokon Fubara ya kada kwamitin bincike saboda girman zarge-zarge wanda ya daga hankalin mutanen jihar Rivers."
- Rejoice Okoli
Karin bayani na tafe...
Asali: Legit.ng