Home Back

KIWON LAFIYA: Idan aka rage zazzaɓin Maleriya a Afrika, tattalin arzikin nahiyar zai ƙaru

premiumtimesng.com 2 days ago
Mosquito
Mosquito

Wani rahoto da Cibiyar Daƙile Cutar Maleriya, wato ‘Malaria No More UK’ ta fitar, ya nuna cewa idan Hukumar Lafiya ta Majalisar Ɗinkin Duniya (WHO) ta rage zazzaɓin malariya da kashi 90% bisa 100% nan da shekarar 2030, to nahiyar za ta samu ƙarin bunƙasar tattalin arziki na har zuwa Dala biliyan 126.9.

Rahoton wanda kamfanin samar da magunguna na Gavi ya kwafa ya watsa a shafin sa na yanar gizo a ranar Talata.

Rahoton dai ya tattaro bayanai ne daga bin diddigin da ‘Oxford Economics Africa’ suka yi, tare da cewa muhimmancin rage zazzaɓin maleriya a Afrika ya na da tasirin gaske ga tattalin arzikin nahiyar, musamman ƙarfin arzikin cikin gida (GDP).

Rahoton ya ce tattalin arzikin Najeriya zai iya samun ƙaruwar Dala biliyan 35, sai kuma hada-hada cinikayyar ƙasa da ƙasa za ta bunƙasa da Dala biliyan 80 zuwa 2030.

Sai dai kuma rahoton ya ce zai yi wahala a ce WHO ta samu nasarar kakkaɓe kashi 90% na zazzaɓin maleriya da mace-macen da ke da nasaba da maleriya a Afrika.

Maleriya a cewar rahoton ta na kashe mutum aƙalla 600,000 kowace shekara, inda kashi 95% cikin kashi 100% na waɗanda maleriya ke kashewa a duk shakara, ‘yan Afrika ne, musamman ƙananan yara ‘yan ƙasa da shekaru biyar.

Amma kuma cutar ta maleriya na shafar manya, inda hakan ke haddasa samun kuɗin shiga ga iyalin mamaci da kuma tsadar magunguna.

Rahoton ya ce yaƙi da cutar maleriya a Afrika ya samu cikas sanadiyyar canje-canjen yanayi, faɗace-faɗace, muggan ƙwayoyi, rashin nagartar magungunan kashe ƙwari da kuma cutar korona. Waɗannan kamar yadda rahoton ya nuna, sun haifar tsaikon samun nasarar yaƙi da cutar maleriya a Afirka.

Aƙalla mutum miliyan 249 ke fama da zazzaɓin maleriya a duniya, yayin da mutum 608,000 ke mutuwa a cikin ƙasashe 85.

People are also reading