Rikicin Manoma da Makiyaya Ya Jawo An Kashe Mutane da dama a Jigawa
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Jigawa- Rikicin manoma da makiyaya a jihar Jigawa ya jawo asarar rayukan mutane uku a yankin gandun dajin Baranda da ke karamar hukumar Kiyawa.
Lamarin ya afku ne bayan an samu sabanin fahimta tsakanin makiyaya da manoma a yankin kan saboda furucin gwamnati.
Vanguard News ta wallafa cewa jami'in hulda da jama'a na rundunar 'yan sandan jihar, DSP Lawal Shiisu ya tabbatar da lamarin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Rundunar 'yan sandan Jigawa ta bayyana cewa an samu ceto wadansu da rikicin manoma da makiyaya ya rutsa da su a jihar.
Pulse Nigeria ta wallafa cewa sun ceto mutane uku da raunuka daban-daban, sannan an ceto wasu guda shida da ake dab da kai wa hari.
Jami'in hulda da jama'a na rundunar 'yan sandan Jigawa, DSP Lawal Shiisu ya tabbatarwa Legit Hausa cewa ba a kama kowa ba kan lamarin.
Rundunar 'yan sandan Jigawa ta bayyana cewa yanzu haka ana gudanar da taron kusoshin gwamnati kan rashin fahimtar da ta jawo rikicin manoma a jihar.
DSP Lawal Shiisu Abdullahi ya shaidawa Legit Hausa cewa an samu rikicin ne saboda tunanin gwamnati ta kwace burtalai kuma an mayar da su ga manoma.
Ya ce yanzu haka za a bambance wa makiyayan da manoman wurin da aka kwace a gandun dajin, da wuraren da har yanzu burtalai ne.
A baya mun ruwaito cewa rikicin manoma da makiyaya ya yi sanadiyyar mutuwar mutane akalla guda biyar a jihar Jigawa.
Jami'in hulda da jama'a na rundunar, DSP Lawal Shiisu ya ce lamarin ya afku a dajin Hayin Kogi da ke karamar hukumar Birnin Kudu.
Asali: Legit.ng