Home Back

Amurka ta aike da karin sojoji yankin Gabas ta Tsakiya

dw.com 2024/5/16
Amurka ta aike da karin sojoji yankin Gabas ta Tsakiya
Amurka ta aike da karin sojoji yankin Gabas ta Tsakiya

Wani jami'i a ma'aikatar tsaron Amurka ta Pentagone da ya bukaci a sakaya sunansa ya ce Amurka ta dauki wannan mataki da nufin dakile duk wata barazana ta Iran da kuma kare muradunta a yankin.

Sai dai a daidai lokacin da Washington ta sanar da wannan mataki, ministan harkokin wajen Italiya ya zanta ta wayar tarho da takwaransa na Iran da nufin yayyafa ruwan sanhi ga wannan sabon rikici da ke shirin daukar dumi a yankin Gabas ta Tsakiya.

A cikin wata sanarwa da ya fidda jami'in diflomasiyyan na Italiya Antonio Tajani ya ce ya rarrashi hukumomin fadar Taheran da ta kai zuciya nesa sannan kuma ya bukaci da ta kwantar da hankulan kungiyoyin masu alaka da Iran a yankin da su guji tayar da fitina don kauce wa barkewar gagarumin rikici da ba a san karshensa ba.

People are also reading