Home Back

Albashi: Kungiyar NLC Ta Juyawa Tinubu Baya, Ta Fadi Gaskiyar Halin da Ake Ciki

legit.ng 2024/7/1
  • Ƙungiyar ƙwadago ta NLC ta yi martani kan iƙirarin da shugaban ƙasa Bola Tinubu ya yi na cewa an cimma matsaya kan mafi ƙarancin albashi
  • NLC ta bayyana cewa saɓanin abin da shugaban ƙasan ya faɗa, babu wata yarjejeniya da aka cimmawa
  • Ta dage cewa har yanzu tana nan kan bakanta na sai gwamnati ta biya ma'aikatan Najeriya mafi ƙarancin albashi na N250,000

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Ƙungiyar kwadago ta ƙasa (NLC) ta musanta iƙirarin shugaban ƙasa Bola Tinubu na cewa an cimma matsaya kan sabon mafi ƙarancin albashin ma’aikata na ƙasa.

Ƙungiyar ta dage cewa har yanzu tana kan buƙatar ta na neman a biya N250,000 a matsayin sabon mafi ƙarancin albashi.

NLC ta musanta cimma yarjejeniya da gwamnati
NLC ta dage sai gwamnati ta biya N250,000 matsayin mafi karancin albashi Hoto: @NLCHeadquarters Asali: Twitter

Shugaban ƙasa Bola Tinubu a yayin jawabinsa na ranar dimokuraɗiyya ya nuna cewa an cimma matsaya tsakanin gwamnati da ƴan ƙwadago kan mafi ƙarancin albashin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

NLC ta musanta cimma yarjejeniya da gwamnati

Jaridar Daily Trust ta ce a wata sanarwa a jiya, muƙaddashin shugaban ƙungiyar NLC, Prince Adewale Adeyanju, ya ce babu wata yarjejeniya da kwamitin tattaunawa kan mafi ƙarancin albashin ya cimmawa.

Muƙaddashin shugaban na NLC ya bayyana cewa har yanzu buƙatarsu tana nan a kan N250,000 kuma ba su ga dalilin da zai sanya su rage hakan ba, rahoton jaridar The Punch ya tabbatar.

Meyasa NLC ta musanta iƙirarin Tinubu?

NLC ta ce ta fito ta bayyana hakan ne domin Shugaba Tinubu, ƴan Najeriya da masu ruwa da tsaki su sani, saboda ga dukkan alamu waɗanda suka ba shi bayanai kan tattaunawar, ba su sanar da shi gaskiyar halin da ake ciki ba.

"NLC ta yi tsammanin cewa masu ba shugaban ƙasa shawara za su gaya masa cewa ba mu cimma wata matsaya da gwamnatin tarayya kan abin da za a biya a matsayin mafi ƙarancin albashi ba."
"Mun yi mamaki da shugaban ƙasan ya ce akwai matsayar da aka cimma. Mun yi amanna cewa mai yiwuwa yaudararsa aka yi ya yarda cewa akwai yarjejeniya da NLC da TUC."
"Babu wata yarjejeniya, kuma dole mu sanar da hakan ga shugaban ƙasa, ƴan Najeriya da sauran masu ruwa da tsaki domin kaucewa kawo ruɗani a tattaunawar da ake yi kan mafi ƙarancin albashin."

- Prince Adewale Adeyanju

Matsayar NLC kan N62,000

A wani labarin kuma, kun ji cewa ƙungiyar ƙwadago ta bayyana cewa ba za ta ƙarbi tayin N62,000 ko N100,000 a matsayin sabon mafi ƙarancin albashi na ma’aikatan Najeriya ba.

Ƙungiyar ta haƙiƙance kan cewa sai dai gwamnati ta biya N250,000 a matsayin sabon mafi ƙarancin albashi ga ma'aikatan Najeriya

Asali: Legit.ng

People are also reading