Home Back

Tsaro: Sabon Kwamishinan 'Yan Sandan Kano Ya Umarci Sintirin Jami'ai Babu Kakkautawa

legit.ng 2 days ago
  • Rundunar 'yan sandan Kano ta dauko hanyar magance karuwar ayyukan bata gari da fadan dabanci da yake neman ya dawo a halin yanzu
  • Sabon kwamishinan 'yan sandan jihar, CP Garba Salman ya ba jami'ansa umarnin su rika sinitiri a kullu yaumin kuma a kowane lokaci
  • Haka kuma ya umarce su su tabbata sun amsa duk wani kiran neman agaji saboda ayyukan bata gari a sassan jihar domin inganta tsaro

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano- Fargabar karuwar ayyukan rashin tsaro a Kano ya sa sabon kwamishinan rundunar yan sandan jihar, CP Salman Garba ya umarci jami'ansa da gudanar da sintiri a kowane lokaci.

CP Salman Garba ya bayar da umarnin ne a ranar Talata yayin wani taro da shugabannin gudanarwar rundunar.

CP Salman Garba
Rundunar 'yan sandan Kano za ta kara sintiri domin dakile yiwuwar aikata laifuka Hoto: Abdullahi Haruna Kiyawa Asali: Facebook

Jaridar Punch ta wallafa cewa kwamishinan ya kara da bayar da umarnin jami'ansu su tabbata sun amsa duk wani kira kan rashin tsaro a loko da sakon Kano.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Akwai karuwar laifuka da damina," CP Garba

Kwamishinan 'yan sandan Kano, CP Salman Umar ya bayyana cewa ana samun karuwar aikata miyagun laifuffuka lokacin damina.

Jaridar Vanguard ta wallafa cewa kwamishinan ya bayyana haka ne lokacin da ya ke tattaunawa da jami'ansa kan kare rayuka da dukiyoyin mutanen Kano a hedikwatar rundunar da ke Bompai.

CP Garba Salman ya kuma hori sashen hulda da jama'a na rundunar ya ci gaba da kokarin wayar da kan jama'a domin taimakawa wajen inganta tsaro.

A halin yanzu ana cigaba da kira ga jami'an tsaro su kare dukiya da rayukan al'umma.

Yan sanda sun ragargaji miyagu

A baya mun kawo labarin cewa 'yan sandan kasar nan sun yi nasarar dakile satar mutane a Katsina har sun ceto mutane.

Tun da fari, yan bindigar sun kai harin a ranar Talata lokacin da su ka farmaki wani gida a unguwar Comprehensive Quarters a ƙaramar hukumar Dutsinma.

Asali: Legit.ng

People are also reading