Home Back

Gwamnatin Tarayya Ta Bayyana Ranakun Hutun Babbar Sallah a Najeriya

legit.ng 2024/7/7

FCT Abuja - Gwamnatin tarayya karkashin shugabancin Bola Ahmed Tinubu ta bayar da hutun kwanaki biyu ga ma'aikata domin shagalin bikin Babbar Sallah.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Gwamnatin ta ayyana ranakun Litinin 17 da Talata 18 ga watan Yuni, 2024 a matsayin ranakun da babu aiki domin shagalin Eid El-Kabir ta bana.

Ministan cikin gida, Tunji-Ojo.
Babbar Sallah: Gwamnatin tarayya ta bada hutun ranar Litinin da Talata Hoto: Dr. Olubunmi Tunji-Ojo Asali: Twitter

Ministan harkokin ciki gida, Dakta Olubunmi Tunji-Ojo ne ya bayyana hakan ranar Jumu'a, 14 ga watan Yuni, kamar yadda The Nation ta ruwaito.

Tunji-Ojo ya taya daukacin al'ummar musulmi na gida da na kasashen waje murnar wannan rana ta idin layya.

Ya kuma yi kira ga al’ummar musulmi da su ci gaba da da koyi da kyawawan halaye na zaman lafiya, kyautatawa da sadaukarwa a tsakaninsu da kowa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Har ila yau ya buƙaci su yi amfani da wannan damar wajen rokon Allah SWY ya kawo zaman lafiya da haɗin kai a ƙasar nan.

Asali: Legit.ng

People are also reading