Home Back

Dalibar da aka rika sharara wa mari a makarantar Abuja, ta maka makarantar a Kotu

premiumtimesng.com 2024/5/4
Dalibar da aka rika sharara wa mari a makarantar Abuja, ta maka makarantar a Kotu

Dalibar da aka ci zarafinta a makarantar Lead British International School da ke Abuja, Namtira Bwala, ta yi barazanar daukar matakin shari’a kan makarantar idan har ta kasa hukunta wadanda suka ci zarafinta.

Ta kuma bukaci mahukuntan makarantar da su gaggauta yin bincike tare da bayyana tsauraran hukunci akan daliba da suka ci zarafinta da suka hada da Maryam Hassan, Faliya, da wasu dalibai tara.

A wani Bidiyo da ya karade shafukan yanar gizo an ga yadda Maryam Hassan da wata Faliyat suke sharara wa Namtira mari saboda zargin hirar saurayi.

An rufe makarantar saboda lamarin. Ministan harkokin mata, Uju Kennedy-Ohaneye ne ta bayar da umarnin rufewar ranar Talata.

Sai dai a wata wasika ta hannun lauyoyinta, Deji Adeyanju da Partners, dalibar da aka zalunta ta ce idan har mahukuntan makarantar suka kasa hukunta masu wadannan dalibai a cikin sa’o’i 48 da samun takardar, makarantar za ta yaba wa aya zaki.

“Wanda muke karewa da wasu iyaye da dama da ke makarantar Lead British International School sun sanar da mu, kuma mun yi imani da su, cewa wannan ta’asa ta ci gaba da faruwa a makarantar. Wanda muke wa aiki na cikin firgici da tsoro har yanzu saboda irin ta’asar da dalibai masu cin zali suke wa wadanda suke fi karfi a makarantar.

Bayan haka Dalibar ta hannun lauyoyinta sun bayyana cewa makarantar ba ta nuna damuwarta game da wulakanci da cin zarafin yarinyar da ka yi ba. A dalilin haka lallai za su garzaya kotu domin a bi mata hakkin ta.

People are also reading