Kungiyar Kwadago Ta Bayyana Matsayarta Bayan Sabon Karin Kudin Wuta
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Nigeria - Kungiyoyin kwadago sun nuna rashin jin dadi kan yadda kamfanoni suka kara kudin lantarki a Najeriya.
A jiya Laraba ne kungiyar kwadago ta yi magana kan karin kudin da aka yiwa wadanda suke layin Band A.
Jaridar Punch ta ruwaito cewa kamfanoni masu rarraba wutar lantarki sun yi bayani kan dalilin karin da aka samu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kungiyoyin kwadagon NLC da TUC sun yi Allah wadai da karin kuɗin lantarki da kamfanonin rarraba wuta suka kawo a cikin makon nan.
Yan kwadago sun ce har yanzu suna kira ga gwamnatin tarayya kan rage kudin wuta kuma wannan karin bai kamata ba, rahoton New Telegraph.
A ranar Litinin da ta wuce ne kamfanonin rarraba wuta suka kara kudin lantarki ga yan layin Band A daga N206.80 zuwa N209.50.
Kamfanonin da suka kara kudin sun hada da kamfanin raba wuta na Ibadan, Kaduna, Legas da sauransu.
Kamfanonin sun ambaci tashin dala, karuwar farashin kayayyaki da gas cikin dalilan da suka janyo karin kudin.
Duk da karin kudin, kamfanonin sun bayyana cewa za a cigaba da samun wutar lantarki yadda ya kamata a garuruwan Najeriya.
A wani rahoton, kun ji cewa ministan makamashi, Adebayo Adelabu ya caccaki masu sukar gwamantin tarayya kan karin kudin lantarki ga 'yan sahun Band A.
Ministan ya ce maganar cewa karin kudin wutar ya jawo tashin kudin kayan masarufi magana ce da ba za ta kama hankali ba.
Asali: Legit.ng