Home Back

Zamu yi fito na fito da masu shirin tada tarzoma ~ Kwamishinan ƴan sandan Kano

dalafmkano.com 2024/9/28

Rundunar ƴan sandan jihar Kano ta ce a shirye take wajen yin fito na fito da dukkan waɗanda suke yunƙurin tayar da tarzoma wajen cimma burikan su, tare da ɗaukar matakin doka.

Kwamishinan ƴan sandan jihar Kano CP Muhammad Usaini Gumel, ne ya bayyana hakan yayin taron manema labaran da ya gudanar yau, a hedikwatar rundunar da ke Bompai a jihar Kano, tare da gammayar jami’an tsaro a jihar.

Ya ce duk wanda yake tunanin zai kawo tasgaro wajen lalata kyakkyawan zaman lafiyar da ake da shi, rundunar za tayi duk abinda ya dace dan ganin jihar Kano ta zauna lafiya.

CP Gumel, ya kuma gargaɗi dukkanin masu yunƙurin tayar da tarzoma da su guji yin hakan domin ba za ta lamunci hakan ba.

“Muna gargaɗar duk wata ƙungiya, ko kuma masu niyyar tayar da tarzoma da su kaucewa yin hakan, domin duk wanda ya shiga hannu wajen tada hankalin mutane zamu kama shi doka kuma tayi aiki a kansa, dan haka kowa ya zauna lafiya, “in ji CP Gumel”.

Wannan dai na zuwa ne bayan da ake zargin wasu na neman tayar da hankalin al’umma wanda hakan ka iya haifar da barazanar tsaro a jihar.

People are also reading