Home Back

Goodluck Jonathan Ya Bayyana Nasara 1 da Najeriya Ta Samu Saboda Dimokuraɗiyya

legit.ng 2024/7/5
  • Tsohon shugaban kasa, Goodluck Ebele Jonathan ya yi jawabi kan cikar Najeriya shekaru 25 kan turbar dimokuraɗiyya
  • Shugaba Goodluck Jonathan ya kuma yi karin haske kan yadda lamura ke tafiya a Najeriya duk da tarin matsalolin ƙasar
  • An ruwaito cewa tsohon shugaban kasar ya yi jawabin ne a fadar sarkin Benin yayin wata ziyara da ya kai a jiya Talata

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Edo - Yayin da ake cika shekaru 25 da dorewar mulkin dimokuraɗiyya a Najeriya, tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya yi bayani.

Shugaba Jonathan ya ce duk da tarin matsalolin da ake fama da su a Najeriya, akwai abin da za ta yi alfahari da shi.

Jonathan
Goodluck Jonathan ya bukaci a cigaba da bin tsarin dimokradiyya. Hoto: Goodluck Ebele Jonathan Asali: Facebook

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa shugaban ya yi jawabin ne jim kaɗan bayan ganawa da Oba Ewuare II a fadarsa da ke Benin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jonathan: "Najeriya ta samu ribar dimokuraɗiyya"

A yayin da yake hira da yan jarida, shugaba Goodluck Jonathan ya ce har yanzu a Najeriya mutane suna da damar tofa albarkacin baki kan lamuran kasar.

Goodluck Jonathan ya ce hakan abin alfahari ne ga yan kasa kasancewar a baya, lokacin mulkin soja, ba haka lamarin yake ba.

A cigaba da bin dimokradiyya

Har ila yau shugaba Goodluck Jonathan ya ce ka da yan Najeriya su yi tsammanin magance matsalolin ƙasar a kankanin lokaci, rahoton Tribune.

Jonathan ya ce gyara abu ne da ke ɗaukan lokaci mai tsawo kafin a cimma shi, saboda haka a cigaba da ƙoƙarin tafiya kan tsarin dimokuraɗiyyar har a kai inda ake so.

Oba Ewuare II ya godewa Jonathan

Goodluck Jonathan ya je Benin ne domin ƙaddamar da wani taro da zai jagoranta a jihar Edo sai ya garzaya fada domin neman albarkar sarki.

Saboda haka Oba Ewuare II ya mika godiya ga tsohon shugaban kasar bisa girmama fadar da yake yi a kowane lokaci.

Gwamnati ta ba da hutun dimokradiyya

A wani rahoton, kun ji cewa ministan harkokin cikin gida, Hon. Olubunmi Tunji-Ojo ya ayyana ranar Laraba 12 ga watan Yuni a matsayin ranar hutu ga 'yan Najeriya.

Rahotanni sun nuna cewa 12 ga watan Yuni na kowace shekara gwamnatin tarayya ta tsayar domin yin bikin murnar zagayowar ranar dimokuradiyyar Najeriya.

Asali: Legit.ng

People are also reading