Goodluck Jonathan Ya Bayyana Nasara 1 da Najeriya Ta Samu Saboda Dimokuraɗiyya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Edo - Yayin da ake cika shekaru 25 da dorewar mulkin dimokuraɗiyya a Najeriya, tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya yi bayani.
Shugaba Jonathan ya ce duk da tarin matsalolin da ake fama da su a Najeriya, akwai abin da za ta yi alfahari da shi.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa shugaban ya yi jawabin ne jim kaɗan bayan ganawa da Oba Ewuare II a fadarsa da ke Benin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A yayin da yake hira da yan jarida, shugaba Goodluck Jonathan ya ce har yanzu a Najeriya mutane suna da damar tofa albarkacin baki kan lamuran kasar.
Goodluck Jonathan ya ce hakan abin alfahari ne ga yan kasa kasancewar a baya, lokacin mulkin soja, ba haka lamarin yake ba.
Har ila yau shugaba Goodluck Jonathan ya ce ka da yan Najeriya su yi tsammanin magance matsalolin ƙasar a kankanin lokaci, rahoton Tribune.
Jonathan ya ce gyara abu ne da ke ɗaukan lokaci mai tsawo kafin a cimma shi, saboda haka a cigaba da ƙoƙarin tafiya kan tsarin dimokuraɗiyyar har a kai inda ake so.
Goodluck Jonathan ya je Benin ne domin ƙaddamar da wani taro da zai jagoranta a jihar Edo sai ya garzaya fada domin neman albarkar sarki.
Saboda haka Oba Ewuare II ya mika godiya ga tsohon shugaban kasar bisa girmama fadar da yake yi a kowane lokaci.
A wani rahoton, kun ji cewa ministan harkokin cikin gida, Hon. Olubunmi Tunji-Ojo ya ayyana ranar Laraba 12 ga watan Yuni a matsayin ranar hutu ga 'yan Najeriya.
Rahotanni sun nuna cewa 12 ga watan Yuni na kowace shekara gwamnatin tarayya ta tsayar domin yin bikin murnar zagayowar ranar dimokuradiyyar Najeriya.
Asali: Legit.ng