Home Back

Mun Fara Raba ‘Yan Bindiga Da Makamai A Filato – Gwamna Muftaang

leadership.ng 2024/5/20
Mun Fara Raba ‘Yan Bindiga Da Makamai A Filato – Gwamna Muftaang

Gwamnatin Jihar Filato, ta ce ‘yan ta’addan da suka addabi karamar hukumar Wase, sun mika mata bindigunsu kirar AK-47 da dama.

Mai taimaka wa gwamna Caleb Mutfwang na jihar a bangaren tsaro da kuma shugaban rundunar Operation Rainbow, Birgediya Janar Gakji Shippi ne, suka bayyana haka a yayin wani taron manema labarai da suka gudanar a Jos babban birnin jihar.

Janar Shippi, ya bayyana cewar mika makaman da ‘yan bindigar suka yi, ya biyo bayan tattaunawar da aka yi tsakaninsu da gwamnatin jihar.

Ya ce baya ga bindigu kirar AK-47, akwai wasu nau’ikan makamai da ‘yan bindigar suka mika wa gwamnatin jihar, matakin da ya ce ya nuna irin kokarin da gwamnati ke yi wajen raba al’umma da makamai.

Kwamandan rundunar Operation Rainbow, ya ce ana ci gaba da kokarin ganin wasu karin ‘yan bindigar sun mika makamansu ga gwamnati, don rage yawaitar kai hare-hare a karamar hukumar Wase.

Jihar Filato dai na daga cikin jihohin da ke fuskantar matsalar tsaro, rikicin kabilanci da rikicin addini a Nijeriya.

A baya-bayan nan rikicin kabilanci a jihar ya yi sanadin salwantar rayukan gomman mutane, lamarin da ya kai gwamnatin jihar ayyana dokar ta baci a wasu yankuna.

A idan ba a manta ba jihohi irin su Katsina, Zamfara da Neja duk sun yi irin wannan yunkuri na ganin an yi Sulhu tare da raba ‘yan bindiga da makamai a Jihohin, amma shirin bai yi tasiri ba.

People are also reading