Back to the last page

Waiwaye: Za a fara koyar da yara da harshen gida, gwamnati ba za ta ƙara kuɗin fetur ba a yanzu

bbc.com 13 minutes ago

Wannan maƙalar ta duba wasu daga cikin muhimman abubuwan da suka faru a Najeriya a makon da muke bankwana da shi.

Asalin hoton, Facebook/UNICEF

Majalisar ministoci ta gwamnatin Najeriya ta amince da wata manufa kan amfani da harsunan kasar wajen koyar da dukkan daliban kasar a matakin firamare a fadin kasar. 

Ministan Ilimi Adamu Adamu ne ya sanar da haka ga manema labarai, bayan taron majalisar ministoci da aka yi a ranar Laraba.

Ya ce majalisar ta amince a aiwatar da sabon tsarin amfani da harsunan gida da ake kira National Language Policy wanda ma’aikatarsa ta kirkiro. 

Ministan ya bayyana cewa ” ka'idojin koyarwa na shekaru shida na farko a makaruntun firamare za su kasance cikin harshen gida.”

Tun kafin Najeriya ta samu 'yancin-kai daga Birtaniya take amfani da Ingilishi  a matsayin harshen hukuma inda cibiyoyin ilimi a kowa ne mataki suke amfani da shi a matsayin harshen gama-gari na koyarwa.

Danna nan domin karanta cikakken labarin:

Asalin hoton, Getty Images

Gwamnatin Najeriya ta ce ba ta da niyyar ƙara kuɗin man fetur "a wannan lokaci" yayin da 'yan ƙasar ke ci gaba da fama da dogayen layi a gidajen man.

Wata sanarwa da hukumar kula da rarraba fetur ta NMDPA ta fitar ta ce ya zama dole su musanta jita-jitar da ake yi game da farashin man da kuma ƙarancinsa a cikin Najeriya.

Sanarwar ta ce kamfanin mai na Najeriya, NNPC Limited, ya tanadi man fetur da zai isa amfanin ƙasar tsawon kwana 34.

"Ana bai wa 'yan kasuwa da sauran jama'a shawarar su daina fargaba da kuma sayen man don karkatarwa da kuma ɓoye shi," in ji NMDPR.

Bisa al'ada, akan fuskanci ƙarancin man fetur a duk ƙarshen shekara a Najeriya duk da cewa a baya-bayan nan ba a ga hakan ba sakamakon ƙarin kuɗin man da gwamnati ta dinga yi akai-akai.

Sai dai wannan karon an fara ƙarancin fetur ɗin tun daga tsakiyar 2022, inda wasu gidajen mai ke sayar da lita ɗaya kan N200 zuwa N250 maimakon N185 farashin gwamnati.

Matar Shugaban Najeriya Aisha Buhari ta janye ƙara da kuma tuhumar da take yi wa ɗalibin nan Aminu Muhammad, kamar yadda lauyansa ya shaida wa BBC Hausa.

Cikin wani saƙon tes, Barista C.K. Agu bai yi ƙarin bayani ba game da dalilin da ya sa Aisha ta janye ƙarar.

Matakin na zuwa ne bayan ɗalibin, wanda ke karatu a Jami'ar Tarayya da ke Dutse, ya shafe kwana uku a gidan yari da ke Suleja bisa umarnin kotun bayan ya ƙi amsa laifinsa.

A ranar Litinin ake sa ran ci gaba da zaman kotun don sauraron neman beli da lauyan Aminu ya yi a zaman ranar Talata da aka yi, wanda bai yi nasara ba.

Matar shugaban na zargin Aminu da ɓata mata suna saboda saƙon da ya wallafa a shafinsa na Twitter maƙale da hotonta tare da cewa "ta ci kuɗin talakawa."

Ƙungiyoyin kare haƙƙi da masu sharhi sun soki Aisha game da matakin da ta ɗauka bayan rahotanni sun yi zargin cewa sai da aka lakaɗa wa Aminu duka kafin gurfanar da shi a gaban kotun.

Kazalika, wasu sun soki matashin kan zargin da ya yi wa matar shugaban.

Wata babbar kotun tarayya da ke zama a Minna, jihar Neja, ta bayar da umurnin kama babban hafsan sojin kasa na Najeriya, Janar Faruk Yahaya bisa laifin rashin grimama kotu.

Mai shari’a Halima Abdulmalik, wadda ta yanke hukuncin ta kuma bukaci da a kulle Janar Yahaya a gidan gyara hali na Minna saboda saba ma wani umurnin kotu na ranar 12 ga watan Oktoba, 2022.

Wannan na zuwa ne kwanaki kadan bayan da wata babbar kotun a Abuja ta yanke wa sifeto janar na ’yan sandan Najeriya hukuncin dauri na wata uku saboda kin martaba hukuncin kotu.

Kafin haka, wata kotun ta ba da umarnin kama Abdulrasheed Bawa, shugaban hukumar EFCC mai yaƙi da cin hanci da rashawa.

Shugaba Muhammadu Buhari ya ce gwamanonin jihohin kasar na sace kason kudaden da ake tura wa kananan hukumomi duk wata daga asusun tarayya. 

Shugaban ya yi wannan zargi ne a taron manyan jami'an gwamnati na wannan shekara, na cibiyar nazarin manufofi da dabaru ta kasa (NIPSS) da ke Kuru a Jos. 

A duk shekara dai masu yin kwas a cibiyar, sukan  dauki wani muhimmin lamari da ya shafi kasa baki daya, su yi nazari game da shi, kuma a karshe su gabatar da sakamakon bincikensu da shawarwarinsu.

A bana sun duba batun mulkin kananan hukumomi ne bayan da Shugaban ya ba su umurnin gudanar da nazari a kan yadda ake gudanar da mulkin kananan hukumomi.

Asalin hoton, AFP

Ministan sufuri na Najeriya Mu’azu Sambo ya ce za a yi ƙarin kuɗin tikitin jirgin ƙasan da ke zirga-zirga tsakanin babban birnin ƙasar Abuja, da kuma Kaduna mai maƙwaftaka.

Ministan ya faɗi hakan ne a lokacin da ya gana da manema labaru, sa’ilin da aka yi gwajin jirgin a shirye-shiryen da ake yi na dawo da sufurin.

Ya ce za a yi ƙarin ne bisa dogaro da sauyin da aka samu na tattalin arziƙi.

Ministan ya ce ma’aikatar sufuri na tattaunawa da hukumar lura da jiragen ƙasa ta Najeriya domin ganin ko za a yi ƙarin farashin ne nan take ko kuma za a jinkirta.

Ya ce “kowa ya san cewa farashi ya tashi, hatta farashin tikitin jiragen sama ya tashi, me zai sa mutane su yi surutu idan an ƙara farashin tikitin jirgin ƙasa?”

Asalin hoton, Other

Batun nan na yi wa kasafin kudin 2023 na gwamnatin Najeriya ciko da majalisar dattawan Najeriya ke tuhumar ma’aikatar kudi ta kasar na ci gaba tayar da kura.

Kan wannan batun, Ministar jin kai ta Najeriya aika wa takwararta ta ma’aikatar kudi wata wasika wadda a ciki ta dora alhakin bayyanar wasu naira biliyan 206 cikin kasafin kudin ma’aikatarta, lamarin da ya haifar da ce-ce-ku-ce tsakanin wadannan ma’aikatun gwamnatin biyu.

A makon jiya, yayin da ministar jin kai ta gwamnatin Najeriya ta halarci zaman majalisar dattawan kasar domin kare kasafin kudin ma’aikatarta, wani batu ya taso da ya janyo ce-ce-ku-ce.

Wani mamba na kwamitin ayyuka na musamman na majalaisar dattawan, Sanata Elisha Abbo, ya tambayi Minista Sadiya Farouk yadda – kamar yadda ya ce – yadda wasu bakin naira biliyan 206 suka bayyana cikin kasafin kudin ma’aikatar jin kai, wadda ke ƙarƙashin kulawarta.

Rahotanni a jaridun Najeriya sun ruwaito Minista Sadiya Farouk na dora alhakin bayyanar wadannan biliyoyin nairorin kan ma’aikatar kudi ta kasar.

Lamarin ya kai ga Minista Sadiya Farouk ta rubuta wata wasika kai tsaye ga takwararta, wato ministar kudi Zainab Ahmed, kuma a ciki ta nanata cewa ba ta hannu a wannan kutsen da kudaden suka yi wa kasafin kudin ma’aikatar tata, kuma ta dora laifin haka kan ministar.

To ma’aikatar kudi ta Najeriya ta fitar da wata sanarwa, wadda a ciki ta kare minista Zainab Ahmed daga tuhumar da minista Sadiya Farouk ta yi kan batun.

To idan akwai wani darasi da za a iya cewa na koya, shi ne har yanzu Najeriya ba ta iya kawar da batun nan na yi wa kasafin kudin kasar cuse ba, ta hanyar saka wasu kudade da tun farko ba a amince da su ba a hukumance.

Wani abin da ‘yan Najeriya kuma za su so gani shi ne ko wannan bayanin da ma’aikatar kudin Najeriya ta fitar zai gamsar da majalisar dattawar kasar, da kuma matakin da zai biyo baya.

Hukumar kare hakkin dan adam a jihar Kano ta ce cikin watanni tara sun karbi bayanan aikata fyade har 721 daga sassan jihar.

Shugaban hukumar ya shaida wa BBC cewa cibiyar da ke lura da wadanda aka yi wa fyade da sauran nau’ukan cin zarafin mata mai suna WARAKA ce ta tantance tare da bin diddigin al’amarin.

Fyaɗe, matsala ce da ke ƙara ƙamari a Najeriya musamman yadda ake cin zarafin mata da kananan yara ta hanyar fyaden.

Cibiyar WARAKA ta karbi korafin aikata fyade da sauran nau’ukan cin zarafin mata fiye da dari-bakwai, daga watan Janairu zuwa watan Satumbar shekarar nan.

Hukumar kare hakkin ɗan'adam ta jihar Kano tana aiki kafada-da-kafada da cibiyar ta WARAKA tsawon lokaci kasancewar ta mamba a kwamitin gudanarwar cibiyar.

Bugu-da-kari Malam Shehu ya ce kashi daya cikin uku na korafe-korafen suna gaban kotu, wasu kuma an yanke masu hukunci, amma ya ce akwai wani muhimmin aiki da cibiyar WARAKA ke tallafa wa mutanen.

Matsalar fyade ta jima tana ciwa al'umma tuwo a kwarya musamman a Najeriya, inda fyade bai tsaya a kan manya ba ko 'yan mata, galibi a wannan zamanin an fi cin zarafin kananan yara da jarirai.

Wasu dai na ganin rashin tsattsauran hukunci ga wadanda aka samu da laifin fyade ne yake sanya al'amarin ke kara ta'azzara.

Hukumar tarawa da rarraba kuɗin haraji ta Najeriya - RMAFC ta ce wasu ma'aikatan gwamnati suna karɓar albashin da ya zarta na shugaban ƙasar Muhammadu Buhari.

Shugaban hukumar Mohammed Shehu ya ce "albashin shugaban ƙasa bai kai naira miliyan 1,300,000 ba a wata...kuma ana saka alawus-alawus ɗin shugaban ƙasar ne a cikin albashin nasa."

Ya ƙara da cewa "a yanzu akwai ma'aikata a ɓangaren gwamnati da masu zaman kansu waɗanda suke karɓar irin wannan albashi nunki biyu, ko uku, ko huɗu."

A wani shiri na gidan talabijin na Channels, Shehu ya ce akwai masu karɓar irin wannan albashi a ma'aikatu kamar Hukumar kula da sufurin jiragen ruwa ta Najeriya (NIMASA), da Hukumar sadarwa ta ƙasa (NCC), da Hukumar kula da tashoshin jiragen ruwa (NPA), da kuma Babban bankin Najeriya (CBN) da ma wasu da dama.

Shugaban hukumar ta RMAFC ya kuma ce wasu jami'an gwamnati suna karɓar kuɗin sallama har naira miliyan 500 yayin da shi kuwa shugaban ƙasa yake samun miliyan 10 a ƙarshen wa'adin mulkinsa.

Mohammed Shehu ya ce akwai tsarin biyan albashi guda 17 a ma'aikatu daban-daban a Najeriya.

Daga nan sai ya nuna buƙatar daidaita tsarin yadda ake biyan albashin ma'aikata, inda ya ce bai kamata a samu wani ma'aikaci da ya fi shugaban ƙasa albashi ba.

Back to the last page