Home Back

Kotu ta tabbatar da dokar rushe masarautu biyar a Kano

dalafmkano.com 2024/8/23

Babbar kotun jaha mai lamba 7 karƙashin jagorancin mai shari’a Amina Adamu, ta yanke hukunci akan ƙarar da gwamnatin jihar Kano ta shigar da sarakuna biyar da aka rushe a baya, inda kotun ta ayyana cewar dokar masarautu ta shekarar 2024, wadda majalisar dokokin kano ta yi a matsayin dai-dai.

Da take yanke hukuncin a zaman ta na yau, kotun ta kuma bayyana cewar aikin majalisar dokoki shine ta yi doka, ko ta rushe doka, ko kuma ta yiwa doka gyaran fuska.

Mai shari’a Amina Adamu, ta kuma bayyana cewar Sarakunan Kano waɗanda gwamnati ta cire kada su kara kiran kansu a matsayin sarakuna, kuma su dawo da dukkanin wata kadara mallakin gwamnati wadda take hannunsu.

Har ila yau, kotun ta ayyana cewar jibge jami’an tsaro a gidan sarki na Nassarawa da akayi ya saɓawa doka.

Tun da fari gwamnatin jihar Kano ce ta shigar da ƙarar inda ta roki kotun da ta tabbatar da dokar majalisa ta 2024.

Majalisar dokokin Kano dai ta yi wa dokar masarautu gyaran fuska wanda hakan ya dawo da masarauta guda ɗaya a jahar Kano, wadda ta sanadin rawunan sarakunan Kano biyar, kamar yadda wakilinmu Yusuf Nadabo Isma’il ya ruwaito.

People are also reading