Home Back

Chadi: Kalubalen da ke gaban shugaba Deby

dw.com 2024/7/1
Shugaba Mahamat Idriss Deby

Mahamat Idriss Deby Itno mai shekaru 40 wanda jagoran mulkin Jamhuriyar Chadi ta biyar ta mulkin farar hula bayan gwamnatin wucin gadi na shekaru uku na mulkin sojojin sakamakon mutuwar mahaifinsa, Idriss Deby wakilai na kungiyoyin farar hula da masu fafutuka na yi masa kallo a matsayin wanda ya kai ganasarar da aringizon kuriu. To amma watakila ana ganin inda ya jajirce wajen tabbatar da aiki na gari wa kasarsa killa jama'a sun manta da irin azabar da suka sha a lokacin mulkin da ya yi na soja wanda aka kashe darurrukan rayuka. a lokacin da yake yin jawabi dai ya ce muhimman abinda zai fi bai wa fifiko shi ne ayyukan cigaban kasa.

Kashi 70 cikin dari na kudaden da gwamnati ke kashewa za mu yi amfani da su wajen inganta shaanin illimi da samar da ruwan sha da kiwon lafiya da kuma samar da isashen abinci ta yada ba sai mun yi dogaro ba da wata kasa ba. Mayan shika-shika na tattalin arziki na kasarmu wato noma da kiwo suna cikin tsarinmu haka muna bukatar hanyonyin mota.

Shekaru 30 kenan dai zuriyar Deby na rike da madafun iko a Chadi amma kusan 'yan kasar na cewar rayuwa ba ta sauya ba wa al'umma a duk zamanin mulkin mahaifina har zuwa gwamnatin rikon kwarya to amma wasu manazarta na ganin akwai hanyoyin  samun nasara; sai dai sai ya daure da shi da gwamnatinsa sun nuna sun fi son kasarsu fiye da kawunansu. Max Kemkoye, shugaban wata jamiyya ta siyasa da ke adawa watop UDP.

"Domin fuskantar irin waɗannan ƙalubalen, ana buƙatar hanyoyi ingantatu, waɗanda suka haɗa da ainihin manufa ta siyasa. Sa'annan  muna buƙatar ingantaccen shugabanci tare da kwararru wadanda suka san makamar aiki a gwamnatin domin yi wa al'umma aiki. A baya dai gwamnatin mulkin sojan ta yi kaurin suna wajen murkushe dukkan 'yan adawa na tsawon shekaru uku tare da fitar da abokan hamayyar Janar Deby masu hatsarin gaske daga kada kuri'a".

A ranar 20 ga Oktoba 2022, aƙalla matasa 300 da ke zanga-zangar adawa da mulkin soji da 'yan sanda suka harbe har lahira, a cewar ƙungiyoyin sa-kai na ƙasa da ƙasa. Kana watanni biyu gabanin zaben, Yaya Dillo, dan uwan ​​Mahamat Déby kuma babban abokin hamayyarsa a zaben shugaban kasa, sojoji sun kasheshi a harin da suka kai a hedikwatar jam'iyyarsa. Shin bayan duk wadannan abubuwa yaya Debi zai nemi hanyoyin sake sasanta tsakanin al'ummar kasar Chadin ga abin da Jean-Bosco Manga wani marubucin yake cewa.

"Sai an karfafa tattaunawa idan har ana son a kai ga yin yafiya da sake sansanta tsakanin al umma domin samun hadin kan yan kasar.A lokacin zaben an yi tsananin tashin hankali da rarrabuwar kawunan al'umma sai an dimke wannan baraka.To a yanzu ya kamata dukkanin kabilun kasar a hada da su wajen aikin gina kasa".

Ga wasu masu lura da al'amuran yau da kullum, ɗayan matsalolin farko na aiwatar da waɗannan ayyuka dabam-dabam shi ne kuɗi amma ina kudin suke.  Duk da dimbin albarkatun kasa, Chadi ta kasance daya daga cikin kasashe mafi talauci a duniya, kana tana yin dogara ne kan taimakon kasa da kasa. A kasar ta Chadi dai 'yan adawa na yin korafin cewar kusan yawan arziki kasar na a karkashin mallakar zuriar Deby.

People are also reading