Home Back

‘Yan Bindiga Sun Kashe Mutane 3 A Kasuwa A Zamfara

leadership.ng 2024/5/18
‘Yan Bindiga Sun Kashe Mutane 3 A Kasuwa A Zamfara

Wasu ‘yan bindiga sun kai hari wata kasuwa a garin Tsafe da ke karamar hukumar Tsafe ta jihar Zamfara, inda suka kashe mutane uku tare da raunata da dama.

Wata majiya daga yankin, ta bayyana cewa ‘yan bindigar sun kai hari kasuwar ne da misalin karfe 11 na safiyar Lahadi, inda suka bude wuta kan mai uwa da wabi.

Kakakin rundunar ‘yansandan jihar, ASP Yazid Abubakar, ya tabbatar da faruwar harin.

Sai dai ya ce rundunar ba ta tantance adadin wadanda suka mutu a harin ba.

Kakakin ya kara da cewa an tura karin jami’an hadin gwiwa na sojoji da ‘yansanda zuwa wajen da lamarin ya faru domin fatattakar ‘yan bindigar.

“Muna da labarin harin da aka kai Tsafe, ‘yan bindigar sun shiga garin, an kuma samu asarar rayuka, amma ba zan iya tabbatar da alkaluman ba yanzu.”

Tuni dakarun sojoji da sauran hukumomin tsaro suka yi dirar mikiya a yankin domin tabbatar da tsaro al’ummar da ke rayuwa a yankin.

People are also reading