Home Back

Gwanjon jiragen shugaban kasa za a yi a sayi wasu - Gwamnatin Najeriya

bbc.com 2024/7/3
Shugaba Tinubu

Asalin hoton, OTHER

Yayin da ake ta ce-ce-kuce kan batun sayar da jiragen sama uku na fadar shugaban kasa a Najeriya,gwamnatin ta yi karin haske kan dalilin sayar da jiragen.

Gwamnatin ta ce za a sayar da jiragen ne ba don wani abu sai don su jiragen suna da matsalolin da ke ana yawan kashe kudi wajen gyarasu.

Mataimaki na musamman ga shugaban Najeriya kan harkokin watsa labarai, Abdul'Azeez Abdul'Azeez, ya shaida wa BBC cewa, a lokacin da gwamnatin shugaba Bola Tinubu ta hau mulki sun tarar da manyan jigare a fadar shugaban kasa guda shida da kuma kanana masu saukar ungulu guda hudu.

Ya ce,” A cikin wadannan jirage akwai babba guda Daya wanda shugaban kasa ke hawa, da kuma wasu biyar, kuma a cikin su wadannan jirage yawancinsu ba su da isashshiyar lafiya, musamman ganin cewa an yi shekara da shekaru ana amfani da yawancinsu, ko kuma matsaloli na inji abin da ke janyo ana yawan kashe kudade wajen gyaransu.”

”Wadannan dalilai ne suka sa shugaban kasa ya amince a kan cewa da a yi ta kashe kudade wajen gyara gara a sayar da su.”

Mataimaki na musamman ga shugaban Najeriya kan harkokin watsa labaran ya ce, guda uku za a sayar a cikin jiragen ciki har da wanda shugaban kasa ke hawa.

Ya ce,” Idan aka sayar da jiragen nan uku ciko za a yi a sayi wani mai lafiya wanda ba zair inka bayar da wata matsala ba.”

To sai da kuma hakan na zuwa ne yayin da wani kwamitin majalisar wakilan Najeriyar kan sha'anin tsaro ya bayar da shawarar a sayo wa shugaban kasa wasu jiragen sama biyu, wato na sa da na mataimakinsa.

People are also reading