Home Back

Wane hali kungiyoyin Premier ke ciki kan sabuwar gasar Turai?

bbc.com 2024/5/17
Champions League

Asalin hoton, Getty Images

Ranar Laraba Borussia Dortmund ta yi nasarar cin Paris St Germain 1-0 a wasan daf da karshe a Champions League a Jamus.

Hakan ya kawo barazana ga kungiyoyin Premier League dake fatan samun gurbi biyar a sabon fasalin babbar gasar zakarun Turai da za a fara daga 2024/25.

A wani ma'auni da ake tantance kwazon kungiyoyin Turai wato European Performance Spots - watakila Jamus da Italiya su samu kungiyoyi shida-shida.

A sabuwar gasar da za a fara ta kungiyoyi 36, Borussia Dortmunt ta samu damar daukar lashe Champions League na bana.

Yayin da Roma ko Atalanta watakila daya daga ciki ta yi nasarar daukar Europa League.

Halin da ake ciki a bayyane yake a kungiyoyin Premier League:

  • 'Yan hudun farko a teburin Premier za su shiga Champions League
  • Wadda ta yi ta biyar a teburin Premier za ta shiga Europa League
  • Idan Manchester United ta lashe FA Cup za ta samu shiga Europa League
  • Idan Manchester City ce ta dauki FA Cup, wadda take ta shidan teburin Premier za ta shiga Europa League.
  • Ana sa ran kungiyar da ta kare a mataki na shida da na bakwai a Premier su shiga wasan cike gurbin shiga Conference League.
  • Daga kakar 2024/25 kungiyoyi 36 ne za su buga sabon fasalin Champions League.
People are also reading