Home Back

Gobara ta tashi a Matatar Man Ɗangote

premiumtimesng.com 2024/7/3
Gobara ta tashi a Matatar Man Ɗangote

Gobara ta tashi a Matatar Ɗanyen Mai ta Ɗangote Refinery da ke Legas, kwanaki uku kacal bayan kamfanin ya zargi manyan kamfanonin mai na duniya da ke Najeriya na yi masa zagon ƙasa wajen kasa samun ɗanyen mai.

Ba a dai san abin da ya haddasa gobarar ba, wadda aka nuno ta na ci a shafin Tiwita, wato X, da ke nuna cewa gobarar mai ƙarfi ce sosai, wadda za ta iya yin munmunar ɓarna.

A cikin bidiyon dai an nuno ma’aikatan kamfanin a guruf-guruf a wasu sassan masana’antar, inda wutar ba ta kai can ba.

A cikin farkon Yuni ne Ɗangote ya ce cikin watan Yuli fetur ɗin sa zai karaɗe ko’ina a Najeriya.

Masana na ganin cewa idan Ɗangote ya wadatar da fetur, to farashin sa zai sauka daga Naira 700 zuwa Naira 500. To amma wannan gobara da ta afku a yau Laraba za a iya maida hannun agogo baya.

A ranar Asabar ce Mataimakin Shugaban Kamfanin Fetur da Gas na Ɗangote, Devakumar Edwin ya zargi manyan kamfanonin mai na duniya da ke Najeriya (IOCs) cewa su na yi wa Matatar Ɗangote zagon ƙasa.

People are also reading