Home Back

'Yan kwadago na yajin aikin sai abin da hali ya yi

dw.com 2024/7/3
Hoto: Uwais/DW

Kungiyar kwadago ta Najeriya NLC ta fara yajin aikin sai abin da hali ya yi, bayan tashi baran-baran a tattaunawar da suka gudanar da gwamnatin kasar a daren Lahadi.

Ministan shari'ar kasar ya shaida cewa yajin aikin ya sabawa sashe na 18 na dokokin warware sabani tsakanin ma'aikata da hukumomi, wanda ya yi tanadin bayar da wa'adin kwanaki 15 kafin tsunduma yajin aikin, idan ba haka ba su fuskanci daurin watanni 6 a kurkuku.

karin bayani : Najeriya: Rarrabuwar kawunan 'yan kodogo

Yajin aikin na zuwa ne bayan gaza cimma matsaya kan mafi karancin albashin ma'aikata tsakanin gwamnatin tarayyar Najeriya da NLC din.

People are also reading