Home Back

JANYE YAJIN AIKI: Gwamnati da Kungiyar Kwadago sun cimma matsayar wucin-gadi

premiumtimesng.com 2024/7/3
JANYE YAJIN AIKI: Gwamnati da Kungiyar Kwadago sun cimma matsayar wucin-gadi

Kungiyoyin Ƙwadago na NLC da TUC sun cimma yarjejeniyar dakatar da yajin aiki bayan shafe tsawon dare su na ganawa da wakilan Gwamnatin Tarayya, a Ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya, George Akume a ranar Litinin da dare.

An cimma yarjejeniyar cewa Gwamnatin Tarayya ta amince za ta yi ƙarin mafi ƙanƙantar albashi fiye da Naira 60,000 da a baya ta tsaya, ta ce haka za ta iya biya, kafin tafiya yajin aiki a ranar Litinin.

A taron cimma yarjejeniyar dai har da Mashawarcin Musamman kan Harkokin Tsaro na Shugaban Ƙasa, Nuhu Ribadu da kuma Ministan Yaɗa Labarai, Mohammed Idris.

Shugabannin NLC da TUC sun ce sun janye yajin aiki a ranar Talata, amma sun bai wa Gwamnatin Tarayya kwanaki biyar domin ta cika alƙawarin ƙarin albashin da ta ce za ta ɗora kan Naira 60,000.

Wannan yajin aiki dai tasamu rashin goyon baya daga ƙungiyar Ƙare Haƙƙin Musulmi ta MURIC, wadda ta ce bai kamata a tafi yajin aiki lokacin da Musulmi ke tafiya aikin Hajji ba, kuma lokacin da Babbar Sallah ta gabato.

MURIC tace ‘ba mu yarda a tsunduma yajin aiki lokacin hidimar Babbar Sallah ba’.

Kungiyar Kare Haƙƙin Musulmi da Musulunci wato MURIC, ta ragargaji ƙungiyoyin ƙwadago na NLC da TUC bisa tsunduma tafiya yajin aiki daidai lokacin da hidimar Sallah Babba, wato Id al-Kabir ta gabato.

Shugaban MURIC, Farfesa Ishaq Akintola ya ce MURIC ba ta ce kada a tafi yajin aiki ba, amma a bari sai bayan Babbar Sallah sannan ta tafi.

Shugaban na MURIC ya fitar da wannan sanarwa ce da jijjifin safiyar Litinin, 3 ga Yuni, safiyar da ƙungiyar ƙwadago ta tsunduma yajin aiki.

“NLC ta shirya tafiya yajin aiki a yau Litinin, 3 ga Yuni, 2024. To amma babu tantama kuma ba shakka cewa wannan yajin aiki zai jefa ɗimbin miliyoyin Musulmin ƙasar nan cikin halin ƙuncin shirin Babbar Sallah, wadda ke tafe nan da ‘yan kwanaki kaɗan.

“Kamar yadda aka saba, idan ana yajin aiki, ɓangarori irin su harkokin man fetur da wutar lantarki duk sukan jefa ƙasar nan cikin ruɗani idan suka shiga yajin aiki.

“To shin me NLC ke tunanin zai shafi miliyoyin Musulmin ƙasar nan a lokacin hidimomin Babbar Sallah? Kuɗin motar tafiya gida Sallah na da komawa duk ƙara nunkawa kenan. Zirga-zirga komai kusancin ta daga wannan wuri zuwa wancan, za ta yi matuƙar wahala a lokacin shirye-shirye Sallah da lokacin Sallah har zuwa bayan ta. Dama abin da NLC ke so ya faru kenan?

“NLC ta bada wa’adin tafiya yajin aikin a ɗan ƙurarren lokaci na sa’o’i 48 kaɗai. Irin yadda shugabannin NLC na yanzu ke tunkarar komai gaba-gaɗi ba tare da zurfin tunani ko aiki da hankali da hangen nesa ba, ƙarfafa ce, izgilanci ne kuma girman kai ne, rawanin tsiya.

“Abin da NLC ke yi ƙoƙarin durƙusar da gwamnati ne da gangan, kuma hakan na nuni da cewa ƙungiyar ba ta ganin daraja da ƙimar dokokin tsarin mulkin ƙasa. Kuma ba ta san ƙimar dimokraɗiyya ba.

“Don me NLC za ta tafi yajin aiki lokacin da Babbar Sallah ta kusanto? Shin NLC za ta iya tafiya yajin aiki daidai lokacin da ana saura sati ɗaya Kirsimeti?

“Shin babu ma’aikata Musulmi a cikin NLC ne? Idan akwai mu Musulmi a cikin ƙungiyar, me ya sa NLC ba za ta dubi haƙƙin mu kafin ta yanke shawarar tafiya yajin aikin ba?

“Me ya sa ba za su duba kalanda su ga rashin dacewar tafiya yajin aiki lokacin gabatowar Babbar Sallah ba? Ko kuwa dama su na sane, da wata manufa suka shirya wa Musulmi wannan tsiyar?”

MURIC ta ce ba ta goyon bayan tafiya yajin aiki kafin Babbar Sallah. Sai dai ta ce idan Sallah ta wuce, NLC na da haƙƙin tafiya yajin aiki duk lokacin da ta ga dama.

People are also reading