Home Back

Kotu ta hana 'yan takara 10 tsayawa zaben shugabancin Chadi

rfi.fr 2024/5/4

Kotun tsarin mulkin Chadi ta hana mutane 10 ciki harda manyan 'yan adawa 2 tsayawa takarar kujerar shugabancin kasar, a zaben da za a yi a ranar 6 ga watan Mayun wannan shekarar.

Wallafawa ranar: 25/03/2024 - 08:22

Minti 1

Nassour Ibrahim Koursami dan takarar jam'iyar GCAP, daya daga cikin 'yan takarar da kotun tsarin mulkin Chadi ta hanasu takara.
Nassour Ibrahim Koursami dan takarar jam'iyar GCAP, daya daga cikin 'yan takarar da kotun tsarin mulkin Chadi ta hanasu takara. © AF

Kotun tsarin mulkin kasar ta ce dalilin da ya sa ta hana ‘yan takarar irin su Nassour Ibrahim Neguy Koursami da Rakhis Ahmat Saleh tsayawa zaben, shi ne sun saba ka’ida.

‘Yan takara 10 ne dai za su fafata a zaben, ciki kuwa har da shugaban gwamnatin sojin kasar Mahamat Idriss Deby Itno da Firaministan kasar Success Masra.

Succes Masra, daya daga cikin masu zawarcin kujerar shugabancin Chadi.
Succes Masra, daya daga cikin masu zawarcin kujerar shugabancin Chadi. AFP - -

Janar Deby Itno ya zama shugaban kasar ne a shakarar 2021, bayan mutuwar mahaifinsa Idriss Deby Itno da ya mulki kasar har na tsawon sama da shekaru 30.

Shugaban gwamnatin rikon kwaryar Chadi kuma daya daga cikin 'yan takarar shugabancin kasar a zaben da ke tafe Mahamat Idriss Deby.
Shugaban gwamnatin rikon kwaryar Chadi kuma daya daga cikin 'yan takarar shugabancin kasar a zaben da ke tafe Mahamat Idriss Deby. © AP - Mikhail Metzel

Bayan rantsar da shi dai, ya yi alkawarin mai da kasar kan mulkin dimukaradiya cikin watanni 18, kuma ya tabbatarwa kungiyar Tarayyar Afirka cewa ba zai tsaya takara ba, sai daga bisa bayan tsawaita wa’adinsa da shekaru biyu, ya tabbatar da tsawa takara a zaben.

People are also reading