Home Back

Mutane 2 Sun Shiga Hannu Kan Zargin Su Da Hannu A Sace Mahaifiyar Rarara

leadership.ng 4 days ago
Mutane 2 Sun Shiga Hannu Kan Zargin Su Da Hannu A Sace Mahaifiyar Rarara

‘Yansanda a Jihar Katsina sun cafke wasu mutane biyu da ake zargi da hannu a sace mahaifiyar fitaccen mawakin nan Dauda Kahutu, wanda aka fi sani da Rarara. 

Kakakin ‘yansandan Katsina, ASP Abubakar Sadiq Aliyu, ya bayyana hakan a ranar Juma’a cewa, mutane biyu da ake zargi ana musu tambayoyi.

Ya bayyana cewa a ranar Juma’a 28 ga watan Yuni, 2024, da misalin karfe 1:30 na dare, hedikwatar ‘yansanda ta Danja ta samu rahoton masu garkuwa da mutane sun shiga gidan Hauwa’u Adamu mai shekaru 75 a kauyen Kahutu da ke Jihar Katsina, inda suka sace ta.

DPO din ‘yansanda na yankin Danja ya jagoranci wata tawaga zuwa wurin da lamarin ya faru don kama masu garkuwa da mutanen tare da ceto mahaifiyar mawakin.

A yayin binciken, an kama wasu mutane biyu da ake zargi kuma ana yi musu tambayoyi.

Rarara, shi ne shugaban mawakan shugaban kasa a lokacin gwamnatin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Wakokinsa sun taimaka wajen tara wa shugaba Bola Ahmed Tinubu magoya baya, musamman a tsakanin yankunan Hausawa a Nijeriya.

People are also reading