Home Back

Mutane da dama sun bata sakamakon mummunar ambaliyar ruwa a Australia

rfi.fr 2024/5/19

Ana fargabar mutane da dama sun bace a sakamakon wata mummunar ambaliyar ruwa da ta faru a kasar Australia, lamarin da ya tilastawa kasar sanya dokar tabaci a wasu yankuna.

Wallafawa ranar: 07/04/2024 - 11:22

Minti 1

Irin barnar da ambaliyar tayi a birnin Sydney
Irin barnar da ambaliyar tayi a birnin Sydney AP - Mark Baker

Bayanai sun ce lamarin ya fi muni a yankin kudancin Wales, da kuma arewa maso gabashin birnin Sydney, inda aka kwashe iyalai sama da 300 daga gidajen su, saboda hadarin da suka ciki.

Ma’aikatar bada agajin gaggawa ta bakin minister Catherin King ta ce an sami mummunar asarar rushewar gidaje da manyan gine-ginen gwamnati, da kuma karyewar gadoji a sakamakon ambaliyar ruwan.

Minista Catherine tace har yanzu ana ci gaba da aikin ceto, bayan nasarar gano mutane sama da 200 da ruwa ya so yin awon gaba da su.

Bayan ma’aikatan agaji na gwamnati akwai ma’aikatan agaji na sa kai sama da 500 da suke aikin nemo mutanen da suka bata.

Hukumar da ke sanya idanu kan takaita afkuwar Ibtila’i ta kasar ta ce mummunar guguwar Cyclone ce ta haddasa ambaliyar ruwan, kuma har yanzu akwai garuruwa sama da 60 dake karkashin barazanar shafewa a sanadin ambaliyar ruwan.

People are also reading