Home Back

Hauhawar farashin kayan da ake hasashe a Najeriya ta zarta haka - Masani

bbc.com 2024/7/5
Kayan abinci

Asalin hoton, Getty Images

Masana a Najeriya na ci gaba da tsokaci kan kazancewar hauhawar farashin kayayyaki a kasar.

Masana irinsu Dr Muhammad Shamsudden, malamin tattalin arziki a Jami’ar Bayero Kano, na ganin a zahiri hauhawar farashin kayayyakin ta zarta hakan.

A cikin hirarsu da BBC, masanin tattalin arzikin ya ce akwai dalilai da dama da ke janyo hauhawar farashin kaya a Najeriya, misali a duk lokacin da canjin kudi na kasashen waje ya canja, to kayan da za a siyo daga waje ma farashinsu kan tashi.

Haka idan farashin kayan wajenma ya tashi, mutane kan hakura su koma siyan na gida, kuma idan bukatar kayan gidan ta yi yawa sai kuma farashinsu ya tashi, in ji shi.

Dr Muhammad Shamsudden, ya ce wani daliin da ke sa farashin kaya ya rinka hawa shi ne kara kudaden haraji da ake yawan yi dama kirkiro sabbin haraji.

“ Dama dai a Najeriya akwai matsalar hauhawar farashin kayayyakin sai dai kawai bata kai yadda ake fama ba a yanzu domin akwai dalilan da suka ingiza matsalar, kamar matsalar tsaro inda yawanci yankunan da ake noma a yanzu an daina saboda rashin tsaro.”

Masanin tattalin arzikin ya ce, “ A yanzu duk shekara sai an fuskanci koma baya wajen samar da amfanin gona saboda matsaloli da dama ciki har da tsaro.”

“A don haka yanzu dai ya kamata gwamnati ta dauki matakai da zasu kawo karshen wannan matsala ta hauhawar farashi don da tun farko an yi abin da ya dace, da ba a tsinci kai a cikin yanayin da ake ciki ba a Najeriya.”

Ya ce, dokokin da aka kawo na jari hujja a Najeriya kasar da take ta talakawa ce,ya kamata a sauyasu in ji shi.

Ya ce,” Farfado da darajar naira na daga cikin matakan gyara da ya kamata a dauka don rage matsalar hauhawar farashin kayayyaki.Sai cire tallafi a kan abin da ya shafi makamashi da wutar lantarki da kuma man fetir, sannan ya kamata a daina kara haraji haka kawai, kudin fito ma ya dace a daina kara shi.”

Masanin tattalin arzikin ya ce, idan har aka bi wadannan matakai to ko shakka babu za a samu sauki a game da wannan matsala ta hauhawar farashin kayayyaki a Najeriya.

A rahoton da ta fitar, hukumar kididdiga ta Najeriya ta ce hauhawar farashin kayan abinci ya karu da kashi 44.66 a watan Mayu abin da ya karu daga kashi 24.82 idan aka kwatanta da bara.

Sannan an samu karuwar hauhawar farashin da kusan rabin kashi daya a Mayun idan aka kwatanta da Afrilun 2024.

People are also reading