Home Back

Enyimba, Remo Stars da Rangers Zasu Wakilci Najeriya a Wasannin Afrika

premiumtimesng.com 2024/7/3
Enyimba, Remo Stars da Rangers Zasu Wakilci Najeriya a Wasannin Afrika

A ranar Lahadi ne aka kammala gasar ajin kwararru na gasar firimiyar Nijeriya (NPFL) na kakar 2023/2024, bayan fafata wasannin mako na 38.

Enugu Rangers ce ta lashe gasar bayan haɗa maki 70 a dukkanin wasanni 38 da ta buga, hakan na nufin zata wakilci Nijeriya a gasar zakarun nahiyar Afirka bisa al’ada.

Remo Stars wacce ta kammala gasar a mataki na biyu da maki 65 ita ma zata wakilci Nijeriya a gasar zakarun nahiyar Afirka.

Enyimba kuwa ta samu tikitin wakiltar Nijeriya ne gasa mai daraja ta biyu ta Afrika bayan kammala gasar a mataki na uku da maki 63.

Duk kungiyyar da ta samu nasara a wasan ƙarshe na kofin kalubale na Nijeriya wanda za’a buga tsakanin Abia Warriors da El-Kanemi Warriors za ta bi sahun Enyimba International wajen wakiltar Nijeriya s kofin ƙalubale na Afrika.

Kafin hakan dai an tabbatar da cewa za’a buga wasan karshen ne a ranar 29 ga watan Yuni a filin wasa na Mashoob Abiola dake Abuja da ƙarfe 4 na yamma.

Kawo yanzu dai ƙungiyyar ƙwallon ƙafa ta Ikorodu City,Nassarawa United,
Beyond Limits da El Kanemi Warriors ne suka samu nasarar haurowa zuwa babbar gasar tamola ta Nigeriya (NPFL) ta 2024/2025.

Gombe United, Doma United, Sporting Lagos da Heartland FC ne suka faɗa zuwa gasa mai daraja ta biyu.

Ana kuma tsammanin fara sabuwar kakar wasanni ta 2024/2025 a watan Satumba na 2024 kamar yadda kamfanin dake shirya gasar ya sanar.

Daga Muhammad Suleiman Yobe

People are also reading