Home Back

Abban Kanawa ya baiwa maniyyata Hajjin bana gudunmawar naira N500,000 kowannen su daga gwamnatin jiha

premiumtimesng.com 2024/4/30
DAGA GIDA-GIDA ZUWA GIDAN GWAMNATI: Wane Ne Abba Gida-gida?

Bayan kiraye kiraye da aka ta yi wa gwamnatocin jihohi su cikawa Alhazan bana kudin aikin Hajji, gwamna Abba Yusuf ya ba mara da kun ya inda ya zama zakaran gwajin dafi wajen cikawa Alhazai kudin aikin Haji na bana.

Idan ba a manta ba Fitaccen malami Sheikh Kabiru Gombe ya yi kira ga shugaban Kasa Bola Tinubu da mataimakinsa Kashim Shettima, su wa Allah su agaza wa maniyyata aikin Hajjin bana.

Sheikh Gombe ya yi wannan kira ne a lokacin Tafsirin Azumi da yake yi a Abuja ranar Litinin.

Fitaccen malamin ya ce amfanin nuna cewa musulmai sun zaɓi ‘Muslim-Muslim’ ya yi a Najeriya.

” A halin da ake ciki akwai yiwuwar idan ba gwamnati ta saka baki bane wato ta taimaka wa maniyyata ‘ Ƴan Najeriya ba za su iya zuwa aikin Hajji ba bana.

Hukumar Hajji ta kasa ta sanar cewa nan da kwanaki uku duk wanda bai cika karin naira Miliyan biyu ba kan naira miliyan hudu da ɗaori da ya biya a baya ba, to ba zai samu damar yin aikin Hajji ba bana.

Sannan kuma maniyyacin da bai biya Hajjin ba sai yanzu, naira miliyan 8 da ɗori zai biya.

Bisa haka ne shehin malamin ya yi kira da babban murya zuwa ga shugabanni musamman gwamnonin jihohin Arewa su ba mara ɗa kunya su cika wa maniyyata karin miliyan biyu da Hukumar Hajji ta bijiro musu da shi da rana tsaka don kada su rasa wannan dama na zuwa aikin Hajji a bana.

” Ina gwamnonin mu na Arewa, Ina Abba Gida-Gida, Ina Raɗɗa na Katsina, Ina Zulum na Barno, Ina Bago na Neja, Ina Inuwa na Gombe, Ina Uba Sanin Kaduna, Ku wa Allah ku cika wa maniyyatan jihohin ku kuɗin Hajjin bana su samu su je su sauke Farali.

” Ina da yakinin cewa ko da kowa bai biya wa ƴan jihar sa ba, gwamnan Kebbi zai biya, domin mutum ne da baya barin batu irin haka ya wuce shi.

Baya ga shehin malamin, ƙungiyoyi da dama sun yi irin wannan kira ga gwamnati ta shiga lamarin ta cika wa maniyyata kuɗin aikin hajjin.

Gwamna Yusuf ya tallafawa duk maniyyaci daga jihar Kano naira da 500,000 domin rage kudin da za a cika na domin biyan kudin kujera.

“Da wannan ne maniyyatan da suka yi rajista kuma suka biya jimillar kudin da aka fara biya na Naira miliyan 4.7 da kuma Naira miliyan 4.5 a hukumar alhazai ta jihar yanzu za su ajiye Naira miliyan 1.4 daga cikin karin Naira miliyan 1.9,”

 
People are also reading