Home Back

Gwamnatin Kano Ta Yiwa Alhazan Jihar Babban Gata a Saudiyya

legit.ng 2024/6/29
  • Gwamnatin jihar Kano ta samar da asibiti domin kula da lafiyar Alhazan jihar a ƙasa mai tsarki yayin gudanar da aikin Hajjin bana na shekarar 2024
  • Samar da asibitin a birnin Makkah zai taimaka wajen samar da isashshen kiwon lafiya ga Alhazan jihar da ke Saudiyya
  • Tun da farko gwamnatin jihar ƙarƙashin jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusuf ta ɗauki nauyin likitoci 11 domin kula da lafiyar Alhazan jihar

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kano - Gwamnatin jihar Kano a ƙoƙarinta na samar da isashshen kiwon lafiya ga maniyyatan jihar, ta samar ɗakunan shan magani a birnin Makkah na ƙasar Saudiyya.

Ɗaƙunan shan maganin za su taimaka wajen samar da kiwon lafiyan da ake buƙafa ga Alhazan jihar.

Gwamnatin Kano ta samar da asibiti a Saudiyya
Gwamnatin Kano ta samar da asibiti ga Alhazan jihar a Saudiyya Hoto: Abba Kabir Yusuf Asali: Facebook

Gwamnatin Kano ta samar da asibiti a Saudiyya

Hakan na ƙunshe a cikin wata sanarwa da sakataren yaɗa labaran mataimakin gwamnan jihar, Alhaji Ibrahim Garba, ya fitar a ranar Lahadi, cewar rahoton jaridar Tribune.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanarwar ta ƙara da cewa Amirul Hajj na jihar kuma mataimakin gwamnan jihar, Aminu Abdussalam Gwarzo, ya shirya ziyartar asibitin bayan ya iso daga birnin Madinah, rahoton jaridar The Punch ya tabbatar.

A cewar Alhaji Garba Ibrahim, shugabar ɓangaren lafiya ta hukumar Alhazan jihar, Hajiya Binta Yusuf, ta bayyana cewa asibitin wanda ya samu amincewar hukumomi zai kasance ne a Gida na 5 a Makkah.

An tura tawagar likitoci

Hajiya Binta ta yi nuni da cewa Gwamna Abba Kabir Yusuf ya ɗauki nauyin likitoci 11 ƙarƙashin jagorancin Farfesa Abbas Sheshe domin duba lafiyar Alhazan jihar.

Ta bayyana cewa samar da asibitin ya ƙara nuna shirin da gwamnatin jihar take da shi wajen inganta walwalar Alhazan jihar a ƙasa mai tsarki.

Ta yi nuni da cewa jihar Kano ita ce jiha ɗaya tilo a Najeriya da hukumar NAHCON ta amince ta samar da asibiti ga Alhazanta a Makkah.

Gwamnatin Kano na ciyar da Alhazai

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnatin Kano ta ce tana ba Alhazan jihar da ke ƙasar Saudiyya domin gudanar da aikin Hajjin bana na 2024 abinci kyauta sau biyu a kullum.

Mai magana yawun alhazan jihar Kano kuma kakakin mataimakin gwamnan jihar, Shuaibu Ibrahim ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar.

Asali: Legit.ng

People are also reading