Home Back

Eid Al Adha: Sarkin Musulmi Ya Sanar da Ranar da Za a Yi Babbar Sallah a Najeriya

legit.ng 2024/7/5

Sokoto - Mai alfarma sarkin Musulmi, Alhaji Muhammadu Sa’ad Abubakar III, ya sanar da cewa an ga jinjirin watan Dhul Hijjah a Najeriya da yammacin ranar Alhamis.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sultan kuma shugaban majalisar ƙoli ta harkokin addinin Musulunci a Najeriya (NSCIA) ya ce ranar Jumu'a, 7 ga watan Yuni zai zama 1 ga watan Dhul Hijjah, 1445H.

Sarkin Musulmi, Muhammadu Sa’ad Abubakar III.
Sarkin Musulmi ya sanar da ganin jinjirin watan Dhul Hijjah a Najeriya Hoto: Daular Usmaniyya Asali: Twitter

Wannan na nufin al'ummar Musulmin Najeriya za su yi Babbar Sallah ranar 16 ga watan Yuni, 2024 wanda zai zo daidai da 10 ga watan Dhul Hijjah, Daily Trust ta ruwaito.

Hakan na ƙunshe ne a wata sanarwa da kwamitin duban wata na ƙasa ya fitar ranar Alhamis da daddare ɗauke da sa hannun sakatare, Malam Yahaya Muhammad Boyi.

Malam Yahaya ya ce:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Mai alfarma sarkin Musulmi ya bayyana ranar Jumu'a, 7 ga watan Yuni, 2024 a matsayin ranar 1 ga watan Dhul Hijjah, 1445H."

A ranar Talata ne Sarkin Musulmi ya umurci al'ummar Musulmin ƙasar nan su duba jinjirin watan Dhul Hijjah 1445 bayan faduwar rana a ranar Alhamis.

Legit Hausa ta kawo muku rahoton cewa hukumomi a ƙasar Saudiyya sun sanar da ganin watan Dhul Hijjah tare da ayyana ranar Jumu'a a matsayin 1 ga watan.

Kotun ƙoli ta Saudi Arabia ta tabbatar da haka a wata sanarwa da aka wallafa a shafin Inside The Haramain.

"Ranar Asabar, 15 ga watan Yuni ce za ta kama ranar hawan Arfa yayin da washe gari ranar Lahadi za ta zama ranar Babbar Sallah watau Eid Al Adha."

Asali: Legit.ng

People are also reading