Home Back

1446AH: Gwamnati Ta Ba da Hutu Domin Zuwan Sabuwar Shekarar Musulunci

legit.ng 3 days ago

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Oyo - Gwamnatin jihar Oyo ta ayyana ranar Litinin, 8 ga watan Yuli a matsayin ranar hutu a jihar.

Gwamnatin ta ayyana ranar ne a matsayin ranar hutu domin murnar zagayowar shekarar musulunci ta 1446 bayan Hijirah.

Gwamnatin Oyo ta ba da hutu a jihar
Gwamnatin Oyo ta ba da hutu saboda zuwan sabuwar shekarar musulunci Hoto: Seyi Makinde Asali: Facebook

Hakan na ƙunshe a cikin wata sanarwa da kwamishinan yaɗa labarai na jihar, Prince Dotun Oyelade, ya fitar a ranar Alhamis, 4 ga watan Yulin 2024, cewar rahoton jaridar Leadership.

Ya bayyana cewa gwamnatin jihar ta fahimci muhimmancin da shekarar musuluncin take da shi a rayuwar musulman jihar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya yi kira ga mutanen jihar da su yi amfani da lokacin wajen yin addu'o'in samun zaman lafiya da ci gaba a jihar Oyo da Najeriya baki ɗaya.

Kwamishinan ya kuma buƙaci jama'a da su koyi da abin da ranar take koyarwa tare da haɗa kai domin zama ƴan uwan juna.

"An ayyana ranar Litinin, 8 ga watan Yulin 2024 matsayin ranar hutu domin zuwan lokacin Hijirah, wanda yake nuna Hijirar da Annabi Muhammad (SAW) ya yi daga Makkah zuwa Madina a shekarar 622AD."
"Hijirah lokaci ne na yin tunani, addu'a da son juna. Mu taru a wannan rana domin yin addu'ar samun zaman lafiya, haɗin kai da ci gaba a jihar mu da ƙasar mu."

- Prince Dotun Oyelade

Asali: Legit.ng

People are also reading