Home Back

Rikicin kabilanci ya lakume rayuka a Somaliya

dw.com 2024/6/26
Dan tawaye a Somaliya
Dan tawaye a Somaliya

'Yan sanda a Somaliya sun ce mace-macen ya shafi kabilun Maheren da kuma Dir wadanda ke gaba da juna a lardin Galgadud da ke arewcain kasar, inda akalla mutane 45 suka salwanta..

Wannan dai shi ne rikici mafi muni da aka gani a yankin cikin shekaru, a cewar 'yan sandan a Somaliya.

Fadan da aka kwashe sa'ao'i ana gwabzawa, ya kuma yi sanadin jikkatar wasu kimanin mutum 60.

Al'umar kasar Somliyar da ke rabe cikin manyan da kananan rukunai, galibi na fadawa rikici walau saboda matsaloli na iyaka ko albarkatun kasa da kuma siyasa.

Sa'o'i kafin tashin wannan husumar ne dai, mayakan tarzomar kungiyar al-Shabab suka kai hare-hare kan sansanonin soja hudu duk dai a lardin na Galgadud.

People are also reading