Home Back

Majalisa ƙarƙashina ba ta amince wa El-Rufai ya karɓo bashin dala miliyan 350 ba, ya yi gaban kansa ne – Zailani

premiumtimesng.com 2024/5/3
Majalisa ƙarƙashina ba ta amince wa El-Rufai ya karɓo bashin dala miliyan 350 ba, ya yi gaban kansa ne – Zailani

Tsohon kakakin majalisar Kaduna Yusuf Zailani ya bayyana cewa majalisar Kaduna a karkashin sa ba ta amincewa wa tsohon gwamnan jihar Nasir El-Rufai ya ciwo bashi daga waje ba.

Idan ba a manta ba, PREMIUM TIMES ta buga labarin cewa kakakin majalisar jihar, Yusuf Liman ya kafa wata kwamiti domin ta binciki yadda gwamnatin El-Rufai ya ciwo bashin dala miliyan 350, yadda ta kashe su da kuma kwangilolin da ta yi a lokacin mulkin sa.

Kwamitin za ta gayyaci tsohon kwamishinan kuɗi Mohammed Sani Dattijo da kuma wasu jigajigan gwamnatin Kaduna a lokacin gwamnatin El-Rufai.

Sai dai kuma tsohon Kakakin Majalisar jihar, Yusuf Zailani wanda a baya makusancin El-Rufai ya wanke kansa daga zargin shine ya saka wa tsohon gwamnan jihar hannu ya ciwo bashin..

Zailani ya ce ” Ko da El-Rufai ya buƙaci mu basho dama ya ciwo bashin dala miliyan 350, na ki saka mishi hannu amma ya yi gaban kansa.

Zailani ya ce yana da shaidu har yanzu a majalisar wand sun san da haka.

Ya ce dama likimo ya yi yana jiran wannan rana don ya fallasa abinda El-Rufai ya yi lokacin ya na mulkin Kaduna, yanzu ya samu damar.

Mutanen Kaduna da ƴan siyasa na ci gaba da tofa albarkacin bakin su game da wannan matsala da ta kunno kai a Kaduna mus

People are also reading