Home Back

TCN Ya Kammala Gyaran Wuta a Arewa Maso Gabas Bayan Kwanaki Babu Lantarki

legit.ng 2024/7/3
  • Kamfanin kula da rarraba wutar lantarki na kasa (TCN) ya sanar da kammala gyaran wutar lantarki a yankin Arewa maso gabas
  • A yau Talata, 4 ga watan Yuni kamfanin ya fitar da sanarwar kammala gyaran wanda ɓata gari suka lalata a tsakanin Gombe da Jos
  • Tun ranar 22 ga watan Afrilu wasu ɓata gari suka lalata turakan wuta a yankin wanda ya dauki tsawon lokaci kafin kammala gyarawa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Arewa - Kamfanin rarraba wutar lantarki na kasa (TCN) ya sanar da kammala gyaran wutar lantarki a Arewa maso gabashin Najeriya.

A yau Talata kamfanin ya ba da sanarwar cewa tun jiya Litinin, 3 ga watan Yuni ya kammala hada manyan layukan wutar.

TCN AREWA MASO GABAS
TCN ya sanar da kammala gyaran wuta a Arewa maso gabas. Hoto: Getty Images Asali: Getty Images

Kamfanin ya sanar da kammala aikin ne a shafinsa na Facebook in da ya ce ya kammala gyaran turakan wuta hudu da babban layin wuta daya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yaushe wutar lantarki za ta dawo yankin?

Duk da cewa kamfanin bai ayyana ranar da wutar za ta dawo ba, ya ce a yanzu haka suna shirye su fara aika lantarki ga yankin.

Saboda haka ake sa ran dawowar wutar lantarki a yankin a kowane lokaci daga sa'ar da kamfanin ya fitar da sanarwar.

Me ya kawo jinkirin gyaran wutar lantarki?

Tun ranar 22 ga watan Afrilu da aka lalata turakan wutar, kamfanin ya duƙufa da gyara tare da alkawarin kammala aikin a ranar 27 ga watan Mayu.

Sai dai kamfanin na daf da kammala aikin sai turken wuta daya ya kara lalacewa wanda ya dauki kwanaki kafin sanar da kammala shi a yau.

TCN ya mika godiya ga al'umma

Kamfanin ya mika godiya ta musamman ga gwamnonin yankin Arewa maso gabas bisa hadin kai da suka bayar wajen gyaran.

Har ila yau, ya mika godiya ga al'ummar yankin bisa hakuri da suka nuna na tsawon lokacin da aka yi yayin da ake zaune a duhu.

An yi gyaran wutar lantarki a Abuja

A wani rahoton, kun ji cewa kamfanin rarraba wutar lantarki na Najeriya (TCN) ya sanar da cewa wasu sassa a Abuja sun shafe awanni bakwai ba tare da wuta ba.

A cewar wata sanarwa daga TCN, ya gudanar da aiki kan wasu manyan na'urorin rarraba wutar lantarki a birnin kuma saboda haka ne ya dauke wutar.

Asali: Legit.ng

People are also reading