‘Maido Tallafin Fetur’: Ahmad Gumi Ya Fadi Abin da Zai Kawo Karshen Zanga Zanga
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kaduna - Shahararren malamin addinin Musulunci a Najeriya Sheikh Ahmad Gumi ya kara magana kan dawo da tallafin man fetur a Najeriya.
Sheikh Ahmad Mahmud Gumi ya yi magana ne kan yadda zanga zangar adawa da tsadar rayuwa ke cigaba a fadin Najeriya.
Malamin ya ba shugaba Bola Tinubu shawara kan abin da ya kamata ya yi wajen dawo da tallafi a cikin sakon da ya wallafa a Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sheikh Ahmad Abubakar Mahmud Gumi ya wallafa cewa dawo da tallafin mai ne mafita ga halin da ake ciki a Najeriya.
Malamin ya ce mutane a Najeriya sun kudurta cewa ba wani abu da zai kawo musu sauki sai dawo da tallafi saboda haka ya kamata gwamnati ta sauraresu.
Sheikh Gumi ya ba shugaba Bola Tinubu shawarar dawo da tallafin man fetur na wucin gadi domin saukaka rayuwa.
Ya ce ya kamata a dawo da tallafi na akalla wata shida kafin tsare tsaren da gwamnati ta ce tana yi su fara aiki.
Babban malamin ya ce ya kamata gwamnatin tarayya da duba abubuwan da suka faru a ƙasashen Kenya da Bangladesh domin kaucewa irinsu a Najeriya.
Saboda haka ya buƙaci hukumomin Najeriya da samar da mafita kan halin da ake ciki na tsananin rayuwa da gaggawa domin tsayar da zanga zanga.
A wani rahoton, kun ji cewa matasan Najeriya sun fara zanga zangar adawa da tsadar rayuwa a ranar 1 ga watan Agusta a jihohin ƙasar nan.
Gwamnatin tarayya ta yanke matsaya kan maganar dawo da tallafin man fetur da matasan ke buƙata shugaba Bola Tinubu ya yi.
Asali: Legit.ng