Home Back

Gobara tayi asarar tarin dukiyoyi a wani gidan man Aliko da ke Kano

dalafmkano.com 2024/5/16

Hukumar kashe Gobara ta jihar Kano ta tabbatar ƙonewar wasu gurare daban-daban a gidan Man Aliko da ke kan titin Aminu Kano, bayan da gobara ta kama a ciki a cikin daren jiya Litinin.

Kakakin hukumar kashe gobarar PFS Saminu Yusuf Abdullahi, ne ya tabbatar wa gidan rediyon Dala FM, hakan a yau Talata.

Saminu ya kuma ce daga cikin guraren da suka ƙone akwai ramukan sauke Mai guda 6, da na sauke kananzir, sai kuma rumfar gidan man, haɗi da kawunan zuba Mai baki ɗaya, da kuma baburan hawa guda biyu waɗanda suka ƙone ƙurmus.

Ya kuma ce motar da take ɗauke man an samu fitar da ita ba tare da wutar ta ƙona ta ba, yana mai cewa jami’an nasu sun samu nasarar daƙile gobarar ba tare da ta tsallaka zuwa maƙotan gidan man ba.

“Wutar ta tashi ne yayin da ake sauke Mai, daga cikin motar dakon Man zuwa cikin ramun da ake sauke shi, lamarin da wutar ta yi asarar dukiyoyi da dama, “in ji PFS Saminu”.

Hukuma kashe gobarar ta jihar Kano ta kuma ƙara da cewa sun yi amfani da motocin kashe gobara guda biyu, domin kashe wutar, ɗaya babbar hedkwatar hukumar kashe gobara da ke gidan Murtala, ɗayar kuma daga Rijiyar Zaki.

People are also reading