Home Back

Sarkin Kano Sanusi II Ya Yi Maganar Farko Bayan Yanke Hukunci a Shari'ar Aminu Ado

legit.ng 2024/7/6
  • A karon farko tun bayan nada shi sarkin Kano na 16, Malam Muhammadu Sanusi ya magantu kan halin da Najeriya ke ciki da ma kokarin komawa tafarkin mulkin firaminista
  • Sarki Sanusi II na ganin sauya tsarin mulki ba shi ne zai magance matsalolin da su ka dabaibaye Najeriya a halin da ake ciki ba, inda ya ce ko a da an yi tsarin firaministan
  • Haka kuma Sarkin ya ga rashin dacewar katsalandan da gwamnatin tarayya ke yi cikin mulkin jihohin kasar nan, musamman kan batun masarautun gargajiya

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano – Tun bayan nada shi Sarkin Kano na 16, a karon farko Malam Muhammadu Sanusi II ya yi magana kan halin da kasar nan ke ciki da ma hanyoyin da za a kawo gyara.

A wani labari da ya kebanta da Vanguard News, sarki Sanusi ya lissafa wasu abubuwa da ya ke ganin aiwatar da sub a zai haifar da da mai ido ga Najeriya ba.

Sanusi
Sarkin Kano na 16 Muhammadu Sanusi II ya yi magana kan halin da Najeriya ke ciki Hoto: Sanusi Lamido Sanusi Asali: Facebook

A makon da ya gabata, ‘yan majalisun kasar nan sun fitar da kudurin da zai ba wa Najeriya damar komawa kan tsarin mulkin firaminista maimakon wanda ta ke kai na shugaba mai cikakken iko.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ga jerin wasu daga batutuwan da Sarki Sanusi ya tabo da yadda za su shafi kasar nan;

1. Tsarin mulkin firaminista

Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II ya bayyana cewa komawa tsarin mulkin firaminista ba zai maganta matsalolin da shiyyoyin kasar nan ke fama da su ba.

Ya na ganin Najeriya ta yi fadi da yawa, dauke da kabilu daban-daban a kunshe su a tsarin mulkin firaminisya

2. Menene amfanin Majalisun biyu? Sarki Sanusi

A hirar da ya yi, Sarki Muhammadu Sanusi II ya ce bai ga muhimmancin samar da majalisun kasa guda biyu ba, kamar yadda ake da majalisar wakilai da ta dattawa a Najeriya.

Haka kuma sarkin ya na ganin babu wani amfani a ce dole sai an nada ministan daga dukkanin jihohin Najeriya. A ganinsa irin wadannan na daga matsalolin da ke kawo cikas wajen tafiyar da harkokin jama’a wanda haka ba zai taimakawa mutanen kasar ba.

3. Raba Najeriya zuwa shiyyoyi

Raba kasar nan zuwa shiyyoyi ba shi ne zai dakile matsalar tsaro da sauran matsaloli da jihohin Najeriya ke fama da shi ba a yanzu, a ra’ayin Sarki Muhammadu Sanusi II.

Ya ce kasar nan na da kabilu da dama da ba zai kyautu a matse su cikin shiyya shiyya ba, domin ko a lokacin da ake kan mulkin firaminista, haka aka yi ta kara raba shiyyoyin.

Sarkin ya kara da cewa tun a baya , kabilun Najeriya da ke shiyya daya na kashe junansu saboda bambancin kabila ko al’ada, saboda haka bad ai-dai ba ne a cushe mutane cikin shiyyoyi.

3. FG a jihohi: ‘Bai dace na,’ Sanusi

Sarkin Kano na 16 na ganin gwamnatin tarayya (FG) ba ta kyautawa yadda ta ke tsoma baki cikin al’amuran jihohin Najeriya, musamman kan batutuwan da su ka shafi sarautun gargajiya.

Muhammadu Sanusi II na wannan batu ne a lokacin da ake zargin ‘ a sama’ na da hannu cikin dambarwar sarautar da ta dabaibaye karagarsa da gwamnatin Kano ta kwace daga Sarki na 15, Aminu Ado Bayero.

Sanusi II na ganin kaata ya yi kowa ya tsaya a matsayinsa wajen gudanar da mulki kamar yadda tsarin mulkin kasa ya bayar da dama.

A ganinsa, duk da matsalolin da dimukuradiyya ke tattare da si, ya fi tsarin mulkin firaminista.

4. Yadda za a magance matsalolin Najeriya

Daya daga hanyoyin da Sarkin Kano Muhammadu Sanusi ke ganin za a magance kasar nan shi ne shugabanni su daina son zuciya tare da mutunta dokar da tsarin mulkin kasa ya samar.

Na biyu shi ne su daina cin dunduniyar jama’a ta hanyar amfani da bambamcin kabila ko addini su na rura wutar gaba da kyashi da tsana saboda biyan bukatar kawunansu.

Sarkin Kano ya shawarci iyaye

A baya mun kawo muku labarin cewa sarkin Kano na 16, Malam Muhammadu Sanusi II ya shawarci iyaye da su sanya idanu kan shige da fice 'ya'yansu da wadanda ke mu'amalantarsu.

Sarkin ya nanata cewa iyaye su na da muhimmiyar rawa da za su taka a rayuwar 'ya'yansu domin su zama mutane na gari a cikin al'uma.

Asali: Legit.ng

People are also reading