Home Back

Man United ta kammala ɗaukar Zirkzee daga Bologna

bbc.com 2024/8/25
 Joshua Zirkzee

Asalin hoton, Getty Images

Manchester United ta kammala ɗaukar ɗan wasan tawagar Netherlands da Bologna, Joshua Zirkzee kan £36.54m.

Tuni mai shekara 23 ya saka hannu kan ƙunshin ƙwantiragin kaka biyar a Old Trafford da cewar za a iya tsawaita masa wata 12, idan ya taka rawar gani.

Zirkzee ya zama na farko da United ta ɗauka tun bayan da Sir Jim Ratcliffe ya mallaki wani kaso mai tsoka a United a cikin Disambar 2023.

Ya ci ƙwallo 12 a wasa 37 a bara a Serie A tare da Bologna, wadda ta samu gurbin buga gasar Champions League a bana.

Zirkzee ya je Bayern Munich daga Feyenoord a 2017 daga nan ya koma Bologna kan yarjejeniyar kaka biyar kan £7.15m, bayan da ya buga wasannin aro a Parma da Anderlecht.

Yana cikin ƴan wasan da Ronald Koeman ya gayyata Euro 2024, amma wasa biyu ya shiga canji, inda Netherlands ta yi rashin nasara a hannun Ingila a daf da karshe.

United ta samu giɓi a gurbin masu cin ƙwallaye, bayan da Anthony Martial ya bar ƙungiyar a karshen watan Yuni, wanda yarjejeniyarsa ya kare.

Rasmus Hojlund, wanda United ta ɗuka kan £72m daga Atalanta a 2023 ya ci mata ƙwallo 16 a wasa 43 da ya buga a kakar da ta wuce.

To sai dain ɗan wasan Denmark ya rasa gurbinsa a karshe-karshen kakar, bayan da Erik Ten Hag ya koma amfani da Bruno Fernandes a gurbin, musamman a FA Cup da United ta doke Manchester City cikin watan Mayu.

People are also reading