Home Back

Sharhin Littafin Zube Na ‘Sidi Ya Shiga Makaranta’ Na Umaru Ladan Da Michael Crowder (2)

leadership.ng 2024/6/30
Sharhin Littafin Zube Na ‘Sidi Ya Shiga Makaranta’ Na Umaru Ladan Da Michael Crowder (2)

Ci gaba daga makon jiya

A shafi na biyar sakin layi na farko an rubuta gabatad da, maimakon gabatar da. Koda yake akan samu irin wannan naso na sautuka a wajen furuci.

A sakin layi na uku an manta ba a sa ayar tambaya ba inda aka ce ‘Mene ne kuma Baturen Makaranta’

A sakin layi na biyar Malam Tanko ya yi amfani da tsarin jimlar harshen Ingilishi inda yake cewa “Mai girma Hakimi, Mai’unguwa Domoso, Manya da sauran jama’an gari……..” Maimakon “Mai girma Hakimi, da Mai Unguwa Domoso, da Manya da sauran jama’ar gari…” A lura cewa digo uku ake yi ba digo tara ba.

Sai can cikin sakin layi na karshe inda aka rubuta ‘Makaranta daya ce tak a Raki, garin Hakimi’ Maimakon ‘Makaranta daya ce tal a Raki, garin Hakimi’ Tal daban, Tak daban.

Sai shafi na shida sakin layi na farko inda aka rubuta ya ke, maimakon yake. Sai kuma sakin layi na biyu da aka rubuta in ji, maimakon In ji. Har ila yau a wannan sakin layi an rubuta sabbin ajujuwa, maimakin sabbin azuzuwa. Kodayake a wani karin harshen Hausar ta yi daidai domin akan samu sauye-sauyen wajen jam’i. misali kaza, jam’inta kaji. Z ta koma J. saboda haka Z na rikidewa ta koma J, ita ma J kan rikide ta koma Z.

A dai sakin layin na biyu an rubuta daukan, maimakon daukar. A sakin layi na uku ya kamata a rubuta ‘Ba shakka Sidi ya taba jin labarin…’ Sai aka rubuta ‘Ba shakka ya taba jin labarin…’ A sakin layi na biyar a karshen jimla ta farko an manta ba a sa ayar tambaya ba. A karshen sakin layin an rubuta ne maimakon ce. Idan an ambaci Allah, a wajen wakilin suna da ke biyo baya ana rubuta y maimakon Y.

A sakin layi na shida an rubuta Kolejin, maimakon Kwalejin. Sai sakin layi na karshe da aka rubuta ‘mai manyan soraye, karauka, da Fadar Sarki da ta Gwamna’ Maimakon ‘mai manyan soraye da karauka da Fadar Sarki da ta Gwamna’

A shafi na tara jimla ta farko an rubuta tsa kanin, maimakon tsakanin. A sakin layi na biyu an rubuta mini, maimakon mun.

Sai sakin layi na uku da aka rubuta: Ya dubi sauran mutanen, idanunsa a zare, kamar Dan Anace, Sarkin dambe, da ya yi tsaye yana tsima bayan ya rotse abokin fadansa kasa yana jiran wani mai giggiwa.

Ni dai na san Dan Anace makadin dambe ne amma ba sarkin dambe ba. Yana dai yi wa shahararrun ‘yan dambe irin su Shago da Dandunawa. Ina kyautata zaton Shago ake son rubutawa aka rubuta Dan Anace.

Sai sakin layi na biyar da aka rubuta fusce, maimakon fusace. Sai ce wa, maimakon cewa. Sai sakin layi na kusa da na karshe da aka rubuta kaimu, maimakon kai mu.

A shafi na goma a karshen sakin layi na dab da na kusa da na karshe an rubuta sa ba, maimakon saba. Sai jimla ta karshe a layin da ta goge ba a san me aka rubuta ba.

Sai shafi na goma sha daya da bai kamata a sa ruwa biyu : a tsakanin makaranta da, ta yo me ba. A shafi na goma sha biyu sakin layi na biyar an rubuta ka ke, maimakon kake. Da ya ke, maimakon yake.

Sai shafi na goma sha uku sakin layi na karshe da aka rubuta “Kafin mu ci gaba da wani zance,

Ya kamata mu isar da farali tukuna.” Maimakon a rubuta “Kafin mu ci gaba da wani zance, ya kamata mu sauke farali.

Sai shafi na goma sha hudu da babu komai a shafin. A shafi na goma sha biyar sakin layi na uku an rubuta ku ke, maimakon kuke. A shafi na goma sha shida sakin layi na biyu an rubuta ta ke, maimakon take. Sakin layi na kusa da na karshe an rubuta kome, maimakon komai. A shafi na goma sha bakwai an rubuta Tun da, maimakon Tunda. Sai sakin layi na karshe jimla ta karshe da aka rubuta Watau, maimakon wato. Kodayake wasu suna da ra’ayin cewa kowanne aka rubuta daidai ne daya Hausar rubuce ce, dayar kuma Hausar baka.

Sai shafi na goma sha takwas kalma ta kusa da ta karshe da aka rubuta zoro, maimakon tsoro. A shafi na ashirin jimlar farko, an rubuta ya ke, maimakon yake. An rubuta karkashin zuciyarsa, maimakon can cikin zuciyarsa. A sakin layi na hudu an rubuta tsabta, maimakon tsafta. Sai a sakin layi na karshe da aka rubuta “Da ranar da aka tsayar ta zo sai aka tafi da Sidi, Musa, da wasu yara biyu…” Maimakon “Da ranar da aka tsayar ta zo sai aka tafi da Sidi, da Musa da wasu yara biyu…”

People are also reading