Home Back

Jami’ar ‘Yar’aduwa Ta Katsina Ta Kama Hanyar Rugujewa – ASUU

leadership.ng 2024/8/21

…Ku Rika Bincike Kafin Ku Yi Magana, Gwamnatin Katsina Ta Mayar Da Martani

ASUU

Jami’ar Umaru Musa Yar’adua da ke Katsina ta kama hanyar rugujewa sakamakon rashin isasun kudaden gudanarwa daga gwamnatin jihar Katsina.

Shugaban kungiyar Malaman jami’a ta ASUU reshen UMYUK Dakta Murtala Abdu Kwara ya bayyana haka a wani taron manema labarai a Katsina.

Ya kara da cewa maganar da ake yanzu jami’ar na kokowa da matsalar rashin wadatattun kudaden tafiyar da bangaren ma’aikata da kuma dalibai.

A cewar Dakta Murtala Abdu Kwara gwamna Malam Dikko Umar Radda na bai wa jami’ar Naira miliyan 7 duk wata a matsayin kudin gudanarwa a maimakon miliyan 16 da ake bata a gwamantin da ta gabata.
“Wannan jami’a ta fara karatu da tsangaya uku ne kacal kuma kudin gudanarwarta miliyan 16 yanzu kuma muna da tsangaya 9 amma kudin gudanarwa ba su canza ba, suna nan miliyan 7” in ji shi

Ya ce halin da jami’ar take ciki a halin yanzu ta sa dole aka dakatar da bai wa wasu sassanta kudaden gudanarwa.

Haka kuma ya koka a kan yadda Gwaman Dikko Umar Radda ya ki aiwatar da kaso 25/35 na albashin ma’aikata wanda ya ce wasu jami’o’i tuni sun fara aiwatarwa/

Kazalika Dakta Murtala Abdu Kwara ya yi kira ga Gwamnatin Jihar Katsina ta sake duba tsarin biyan kudaden gudanarwa na jami’ar domin ceto ta daga rugujewa.

…Ku Rika Bincike Kafin Ku Yi Magana, Gwamnatin Katsina Ta Mayar Da Martani

Gwamnatin jihar Katsina ta maida wa Kungiyar Malaman jami’a ta ASUU reshen Jami’ar Yar’adua da ke Katsina martani dangane da ikirarin da ta yi na cewa jami’ar ta kama hanyar durkushewa.

Kwamishinan ma’aikatan ilimi mai zurfi da kula da kere-kere Ferfasa Abdulhamid Ahmad ya maida martanin da cewa ba gwamnatinsu ba ce ta rage kudaden gudanarwar jami’ar ba.

“Wannan gwamnatin karkashin jagorancin Malam Dikko Umar Radda ba ta taba rage ko naira ba daga kudaden gudanarwa da ake ba Jami’ar Yar’adua kuma ba a taba fashin biyan su ba.”in ji shi.

Kwamishinan wanda ya ce shi daya ne daga cikin Malaman jami’ar kafin ya samu mukami ya san duk abin da ke faruwa yana da masaniyar musamman tafiyar da sha’anin jami’ar.

Kazalika ya yi kira ga kungiyar ASUU da ta koma jami’ar ta bincika ta gani daga yaushe ne aka rage wadancan kudaden da suke magana, ba wai su fito a kafafen yada labarai ba suna fadin abin da ba haka yake ba.

Sannan ya kara da cewa babu wanda ya taba rubuta wa gwamnati cewa kudaden gudanarwa da ake ba jami’ar da sauran manyan makarantu ba sa isarsu, babu wanda ya taba sanar da gwamnati.

“Kuma ina son jama’a da su gane, ASUU sun ce adadin dalibai da tsangaya sun karu, to su bayyana wa duniya adadin kudaden shiga da suke samu a yanzu kowa ya sani.

A cewarsa, ko naira daya ba sa ba gwamnatin jihar Katsina, su ke tara kudinsu, su ke kashe su, saboda haka ya ce su je su bincika tun shekarar 2015 aka fara zabtare kudaden gudanarwa na jami’ar da sauran makarantu guda biyar.

Da kwamishinan ya juya kan korafin da kungiyar ASUU ta yi na cewa gwamnatin tarayya ta fara aiwatar da shirin karin albashi na kaso 25/35, ya ce yanzu haka maganar tana kan teburin Gwamna Dikko Umar Radda jira ake ya ba da umarni.

Ya kara da cewa maganar karin albashi da kungiyar kwadago ta bijiro da ita, ta tsayar da batun, amma tuni an gama wannan maganar, yana mai cewa ya sanar da duk manyan makarantun da suke karkashin kulawar ma’aikatarsa, inda aka kwana da inda aka tashi a kan batun karin albashi, amma ba wai an fasa ba ne.

Ferfasa Abdulhamid Ahmad ya ce akwai abubuwa da yawa da gwamnatin jihar Katsina ta shirya yi bangaren ilimi wanda ya ce wasu ba zai fade su ba yanzu, sai nan gaba saboda mahimmancinsu ga jihar Katsina.

Ya kuma kalubalanci jami’ar Yar’adua wanda ya ce Gwamna Dikko Umar Radda ya yi alkawarin cewa duk dalibin da ya fita da digiri mai daraja ta farko zai dauke shi aiki ba tare da bata lokaci ba, amma ya ce kusan wata biyu da yin wannan batu har gobe jami’ar ba ta aiko a rubuce ba tana son a aiwatar da wancan alkawari.

Ya kara da cewa sai dai su daliban ne suka tunkari ma’aikatar ilimi mai zurfi da kula da kere-kere domin jin inda aka kwana, amma daga jami’ar babu wanda ya rubutu a hukumance.

People are also reading