Home Back

An gudanar da taron addu’a da karatun Alqur’ani, dan samun sauƙi daga matsin rayuwa a Kano.

dalafmkano.com 2024/7/3

Yayin da al’umma ke ci gaba da fuskantar halin matsin rayuwa a sassan ƙasar nan, da safiyar wanna rana ne ɗumbin al’ummar jihar Kano suka gudanar da taron addu’a, tare da karatun Alkur’ani mai girma, domin samun sauƙi.

Al’umma da dama ne dai, maza da mata, manya da yara, suka samu damar halartar taron, wanda ya gudana a filin Bajakoli da ke kan titin gidan Zoo yau Asabar a jihar Kano.

Ƙungiya mai tabbatar da zaman lafiya da ci gaban al’umma da samar da aikin yi ta ta ƙasa wato Sustainable Peace, Empowerment and Deplopment Initiative of Nigeria, haɗin gwiwa da majalisar ci gaban matasan Kano, ne suka shirya taron.

Kwamared Idris Ibrahim Makama unguwar Gini, shi ne shugaban ƙungiyar ta SPEDEN, ya ce sun shirya taron ne domin yiwa jihar Kano, da ma arewacin ƙasar nan addu’a, tare da karatun Alkur’ani mai girma, domin samun sauƙi a wajen Allah S.W.T, dan ganin an fita daga cikin halin matsin rayuwar da aka samu kai yanzu a ciki.

“A lokacin taron mun yiwa ƙasa musamman ma Arewa, addu’o’i, domin fita daga halin tsadar kayayyakin masarufi, da na amfanin yau da kullum, da kuma matsalar tsaro da ake fama da ita; kuma Allah ya yi mana maganin waɗanda suka sanya mu cikin ƙuncin rayuwar da aka samu kai a ciki, “in ji shi”.

Majiyar Dala FM Kano, ta rawaito cewa taron ya samu halartar al’umma da dama, kuma ciki har da malamai, da ƴan ƙungiyoyi, da Dattawa, domin yiwa jihar Kano, da ma arewacin ƙasar nan addu’a.

People are also reading