Home Back

Shekara Daya Bayan Emi’lokan, Rayuwa Ta Zama Mai Ban Tsoro A Nijeriya

leadership.ng 2024/6/26
Rayuwa

Yayin da kashi 90 na ‘yan Nijeriya ke farkawa barci kafin wayewar gari don fara neman abin sawa a baki, kudaden albashi na ma’aikatan gwamnati, kudaden fansho na ‘yan fansho, kudaden albashin ma’aikatan yau da kullum da kudin shiga na marasa aikin yi duk sun tsaya cak ga kuma hauhawar farashin kayayyaki. Bisa ga rahoton Kididdigar Kasuwanci (CPI) na Hukumar Kididdiga ta Kasa (NBS), farashin kayayyaki yanzu sun yi tashin gwaron zabi da kusan kashi 33.20 cikin 100 a watan Maris, 2024.

A halin da ake ciki kuma, a manyan titunan Abuja, Kaduna, Kano, Benin, Legas, Ibadan, Fatakwal da sauran garuruwan Nijeriya, mutane cike suke da damuwa da kuma fargaba, al’amuran da ke nuni da rashin jin dadi yayin da ‘yan kasar ke kokawa da tashin farashin kayayyakin masarufi da sauransu. Farashin shinkafa, tumatir, albasa da sauransu duk sun ninka sau hudu ko fiye da haka. Idan ka hada da kudin sufuri, kudin makaranta, kiwon lafiya, haya da sauransu abin sai lahaula.

Wanna yanayi ya kara fitowa fili karara lokacin da wani Fasto ya ce ya dakatar da karbar hadaya ta mako-mako a cocinsa saboda kuncin tattalin arzikin da ake ciki.’

Jajircewa ko kasancewar halin rashin tausayi?
Babu kowa, ko kadan babu wanda ke da hannu wajen samun danyen man fetur mai yawa a Nijeriya, wannan arziki ne daga Allah. Kwatsam da rana tsaka suka ce sun cire tallafin man fetur. A kwanannan kuma suka ce sun cire tallafi daga wutar lantarki duk da cewa ‘yan Nijeriya na fama da duhu sama da shekaru 30.

Asalin wannan duka shi ne rashin sanin yakamata da rashin bin diddigin al’amuran gwamnatocin da suka gabata wanda ya kai ga rashin shiri da gazawar wadanda ke kan madafun iko a Nijeriya a yau.

Ina tiriliyoyin Naira barkatai da aka samu?
Wata kungiya mai suna Statisense, ta ba da haske kamar haka, ya zuwa yanzu, kwamitin rabon kudaden shiga mai suna ‘Federal Accounts Allocation Committee’ ya bai wa gwamnatin tarayya da na jahohi da kananan hukumomi kudi tiriliyan 6.013 kamar haka; tiriliyan 1.67 a watan Janairu, tiriliyan 2.07 a watan Fabrairu, tiriliyan1.123 a watan Maris, da kuma sai kuma tiriliyan 1.150 a watan Afrilu.

Ku je manyan jihohi da kananan hukumomi kar a yi maganar ziyarar yankunan karkara, wannan makudan kudade da aka ware wa sama da ‘yan Nijeriya miliyan 200 domin jin dadin su, tsaro, ilimi, lafiya, noma da dai sauransu, da alama sun yi batan dabo!

Manufofin kudi da kasuwanci marasa daidaituwa
A cikin shekara guda da ta gabata, kwamitin tsare-tsaren kudi na CBN (Monetary Policy Committee) ya gana sau hudu, kuma bai yi komai ba illa kara kudin ruwa sau hudu. Duk da farmakin da aka kai a kasuwar bayan fage da bindigogi, darajar ta yi kasa a gwiwa wajen musayar Dala. A yanzu Dalar Amurka daya tana kwatankwacin 1,480.81 a NAFED, a NAFEM kuma tana kwatankwacin 1,339.33. Wannan duk tsakanin ranakun 24 zuwa 27 ga watan Mayun 2024 ne, yayin da ita kasuwar bayan fage su kuma na cin karen su ne ba babbaka. Alamun dai shi ne Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya rasa mafita.

Wannan faduwar darajar ta kara dagula tattalin arzikin da tuni ya durkushe wanda yake da alaka da rashin iya gudanar da kasafin kudi da kuma rashin hazaka na majalisar tattalin arzikin kasa (National Economic Council).

Bambance-bambancen da ke tsakanin manyan tsare-tsare na gwamnati da yanayin tattalin arziki a kasa ya bayyana. Faduwar darajar , da hauhawar farashin kayayyaki, da matsalolin rashin samar da ababen more rayuwa da rashin bin dokar kasafin kudi duk sun taru sun haifar da mummunan yanayi ga makomar tattalin arzikin Nijeriya.

Ma’iakata ko kuma malalata
Ga dukkan alamu dai matakan da gwamnati ta dauka na maganin wannan yanayi shi ne na nade-nade da ba da mukamai , amma duk da haka wadanda aka nada ba su da kwarewar aiki don dakile durkushewar tattalin arzikin da ake fama da shi, sai dai kawai sun shagaltu da karbar tagomashin mukaman gwamnati da kuma jagorantar lamuran gwamnati wanda zai amfane su kadai.

Wannan ya bayyana ne a ci gaba da mayar da hankali kan yin sabbin nade-nade tare da fadada gwamnatin ba don taimakon al’umma ba ko kuma aiwatar da ingantattun manufofin tattalin arziki da za su kasance kamar daidaita , rage hauhawar farashin kayayyaki da kuma kawo taimako ga ‘yan Nijeriya. Bisa dukkan alamu dai akwai wata kungiya ta bayan fage da ke tafiyar da nade-naden mukaman domin dalilan zabukan 2027, da son kai da kuma rashin hangen nesa mai zurfi.

Gwagwarmayar ceton rai
Talakawan Nijeriya na fama da matsalar rashin abinci mai gina jiki, talauci, raguwar kudin shiga da kuma rashin iya tanadi domin gobe. Ga masu rike da madafun iko kuwa, sun dukufa ne wajen ba da fifikon jin dadinsu a kan jin dadin al’umma yayin da jam’iyyun siyasa da ma’aikatan gwamnati suka fi damuwa da kwato abin da za su iya daga gwamnati maimakon magance matsalolin da ke addabar kasar.

Wan nan dai ita ce gaskiya, ya rage wa ‘yan Nijeriya su ceto rayuwarsu.

Babbar hanyar zuwa babu ko ina
Aikin Titin Lagos-Calabar (wato Lagos-Calabar Coastal Highway) – Fatan mu anan shi ne ba zai kare ba a matsayin “Aikin giwaye”. Yadda kuma zai sauya arzikin ‘yan Nijeriya cikin dare daya kamar yadda cire tallafin man fetur ya haifar da rudani da ruguza tattalin arzikin kasa cikin rana daya ya kasance abin mamaki a gare ni!
Yanayin matatun mai na Nijeriya – Ga alama sun rikide zuwa kayan tarihi kawai da suka dace da gidajen tarihi na kasa.

Kungiyar Kwadago – Wadannan bijiman karnuka ne wadanda sun rasa muryarsu.
Bangaren Wutar Lantarki – Tabarbarewar rashin wuta, almubazzaranci, wawashe dukiyar al’umma da karancin kishin kasa da samar da duhu shi ne babban aikin wannan bangaren.

Bangaren Noma da Kiwon Lafiya – Don rashin sarari, bincikensu sai wani jikon da yardar Allah.

Rashin iya aiki, rashin kwarewa da kuma rashawa
Duk da makudan kudade da aka ware, almubazzaranci, rashin iya gudanar da mulki, da cin hanci da rashawa na ci gaba da kawo cikas ga ci gaba mai ma’ana. Misalai su ne:
Biyan albashin ma’aikatan gwamnati a kan lokaci ya sha banban da jinkiri da rashin isassun kudin biyan fansho ga wadanda suka yi ritaya. Wannan bambance-bambancen yana nuna rashin ingantaccen tsarin aiki da rashin fifiko ga jin dadin duk ‘yan kasa.
Yadda ake kashe makudan kudade wajen sayen motocin alfarma na ‘yan majalisar tarayya da na bangaren zartarwa, da kuma gyaran gidajen shugaban kasa da mataimakinsa a Legas da wuraren ajiye motoci a harabar majalisar dokokin kasar. Wadannan kashe-kashen kudaden sun sha banban da gwagwarmayar rashin kudi da talakawan Nijeriya ke fama da su da kuma gazawar gwamnati wajen bayar da agaji agare su.

Akwai matsala nan gaba
Nijeriya kasa ce da ke kan tsini, yayin da tsadar rayuwa ke kara hauhawa zuwa wata sabuwar kololuwa.

Ayyukan samar da ababen more rayuwa da gwamnati ta yi ikirarin tanayi, na iya kasancewa nagartattun niyyoyi, amma shin za su iya samar da albarkatu na wadata kamar yadda ake fata?

People are also reading