Home Back

JUYIN MULKI: Hedikwatar tsaron Najeriya ta ƙaryata rahoton wai ana shirya kifar da gwamnatin Tinubu

premiumtimesng.com 2024/4/28
Nigerian Soldiers
Nigerian Soldiers

An jawo hankalin hedikwatar tsaron Najeriya kan wani labari da ke SAHARA REPORTERS suka buga ranar Lahadi cewa wai akwai yiwuwar ana shirya yi wa gwamnatin Tinubu juyin mulki.

Rahoton ya kara da cewa a dalilin haka an tsaurara tsaro da kuma ankarar da dakarun da ke gadin shugaban kasa da, fadar gwamnati da su yi shir ko ta kwana

Kakakin Hedikwatar tsaron Tukur Gusau ya ce jaridar ta shirga karya ne babu wani abu mai kama da haka da ya bijiro a fadar shugaban kasa

” Dakarun tsaro na musamman dake gadin shugaban kasa, fadar AsoRock da Abujan kanta tuni na zaune ne cikin shirin ko ta kwana, ba wai don akwai rade-raɗin juyin mulki ba. A kullum suna zaune ne cikin shiri.

Tukur ya kara da cewa a dalilin haka, Hedikwatar tsaron ta umarci hukumomin bincike na kasa da su binciko musabbabin wannan rahoto, sannan kuma su bi diddigin sa.

Ba yan haka ya ce ita kanta hedikwatar tsaron kasa za ta maka Sahara Reporters kotu.

 
People are also reading