Home Back

Dalilin da ya sa na ziyarci Buhari a Daura – Atiku

premiumtimesng.com 2024/7/1
Dalilin da ya sa na ziyarci Buhari a Daura – Atiku

A wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X, Tsohon mataimakin shugaban Najeriya, Atiku Abubakar ya ce ya kai wa Muhammadu Buhari ziyarar ta ranar Asabar ne don taya shi murnar Babbar Sallah.

Sai dai kuma masu yin nazarin siyasa na ganin ruwa fa baya tsami banza, ziyarar na da alaƙa da siyasar zaɓen Najeriya na shekarar 2027 wanda tuni yan siyasa sun fara shiri.

Atiku na jam’iyyar PDP ne ya zo na biyu a zaɓen shugaban kasa bayan shugaba Tunubu.

Duk da cewa ya tafi kotu domin ƙalubalantar sakamakon zaben, bayan hukuncin kotun Atiku ya hakura amma kuma ya koma gefe yana sake sabon shiri.

People are also reading