Zaben 2027: Kitimurmurar da Ke a PDP da LP Ka Iya Zama Silar Nasarar Tinubu a Zabe Mai Zuwa
Salisu Ibrahim ne babban editan sashen Hausa na Legit. Kwararren marubucin fasaha, harkar kudi da al'amuran yau da kullum ne, yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru takwas
Tsakanin zaben shugaban kasan da aka yi a 2023 zuwa yanzu, an ga abubuwa da yawa wadanda da alama za su yi tasiri ga wasu jam'iyyun siyasa a babban zabe mai zuwa na 2027.
Ga wasu jam'iyyun, kamar jam’iyyar PDP da Labour matsaloli ne da ke nasaba da yiwuwar raguwar damarsu ga kaiwa ga nasara a zaben shugaban kasa mai zuwa a 2027.
Ga wasu kuma, kaamr APC da alama akwai lauje cikin nadi da ka iya kwancewa ya bayyana a fili duba da rabuwar kai da ke tsakanin shugabannin jam'iyyar da 'yan siyasar cikinta.
Wannan, ka iya zama silar dura ruwa a cikin shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu a zaben da a yanzu haka 'yan siyasar Najeriya sun fara shiri tsaf.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wannan rahoton ya mai da hankali ne ga rikice-rikicen da ke cikin jam'iyyun PDP da Labour wadanda za su iya yin tasiri a gare su amma a karshe su zama silar nasara ga Shugaba Tinubu, idan ya yanke shawarar sake tsayawa takara a karo na biyu a 2027.
Tun kafin fara batun zabe, jam’iyyar PDP ta fara rasa matsayinta na babbar jam'iyyar adawa a Najeriya, musamman a idon wasu masu sharhi kan harkokin siyasa.
A halin yanzu, kallo ya koma ga tsagin jam'iyyar adawa ta Labour duba da rikice-rikicen da ke cikin PDP.
Wadannan matsaloli dai ka iya zama silar rashin nasarar PDP a zabe mai zuwa da kuma disashewar haskenta a nan gaba kadan.
Da farko dai, lamarin 'yan tawagar G-5 da suka hada da Nyesom Wike, Gwamna Seyi Makinde, Samuel Ortom, Okezie Ikpeazu da Ifeanyi Ugwuanyi, ya haifar da kakkausar gaba a PDP.
Alamu masu karfi na nuna cewa, jiga-jigan siyasar na ta rabar jam'iyyar APC tun gabanin zaben 2023, har ta kai Shugaba Tinubu ya ba Wike mukamin minista duk da kasancewarsa dan PDP.
Baya ga wannan, ana hasashen aukuwar ayyukan cin dunduniyar jam'iyyar PDP daga yankuna daban-daban na jam'iyyar a Najeriya, musamman jihar Rivers.
Hakazalika, a yanzu haka PDP za ta yi zama a ranar 18 ga watan Afrilu, kuma ana hasashen tsaiko tsakanin tsagin Atiku Abubakar da Nyesom Wike.
Wannan rikici ka iya zama wata kafar nasara ga Tinubu, kasancewar ya iya rabewa da 'yan jam'iyyun adawa; batun Wike ne misali mai karfi, rahoton jaridar Vanguard.
Ana ta samun kyawawan labarai masu dadi sosai daga jam'iyyar Labour tun bayan zaben shugaban kasa da ya gabata.
Sai dai, da farko, an samu tsagewar jam'iyyar zuwa bangaren Lamidi Apapa wanda ya dauki jam'iyyar zuwa wasu matakai don tabbatar da jajircewata a shekarar 2023.
Yayin da har yanzu ba a kai ga kashe wutar da ta kunno ba a jam’iyyar, akwai kuma wata wutar da ta kunno kan batun da ya shafi shugabancin Joe Ajaero da NLC, inda a yanzu shugabannin NLC suka ki amincewa da jagorancin Joe Ajaero wasu jiga-jigai
Ya zuwa yanzu dai jam’iyyun PDP da Labour na da matsalolin da dole su warware kafin su iya fuskantar jam'iyyar APC a zaben shugaban kasa mai zuwa nan da shekaru uku.
A wani labarin kuma, kungiyar kwadago ta Najeriya ta shaida wa dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour cewa yana da ’yancin barin jam'iyyar ba wanda zai hana shi.
Kakakin kungiyar NLC, Benson Upah ne ya bayyana hakan a wata hira da aka yi dashi ranar Lahadi.
Shugabannin NLC sun sha alwashin cewa, ba za su huta ba har sai sun tsige Julius Abure a matsayin shugaban jam'iyyar Labour ta kasa.
Asali: Legit.ng