Home Back

Abun da muka sani kan harin da Iran ta kai wa Isra’ila

bbc.com 2024/5/9
..

Asalin hoton, Reuters

  • Marubuci, Tom Spender
  • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News

A karo na farko cikin tarihi, Iran ta ƙaddamar da hari kan Isra’ila.

Da tsakar daren ranar Asabar ne amsa kuwwa ta riƙa ƙara a faɗin Isra’ila, ana ankarar da al’umma su nemi mafaka yayin da aka riƙa jin fashewar abubuwa lokacin da aka kunna shingen kariyar hare-hare ta Isra’ila.

Fashewar makamai a sararin samaniya ta haskaka sassa da dama na ƙasar yayin da kuma ƙasashe ƙawayen Isra’ila suka harbo makamai da kuma jirage marasa matuƙa tun kafin su isa sararin samaniyar ƙasar.

Aƙalla ƙasashe ne tara ne suka shiga cikin harin na ranar Asabar – inda aka harba makamai daga Iran da Iraq da Syria da Yemen, a bangare ɗaya kuma Isra’ila da Amurka da Birtaniya da kuma Faransa suka kakkaɓo su, da kuma Jordan.

Ga bun da muka sani game da harin

Harin ya ƙunshi jirage marasa matuƙa da miyagun makamai masu linzami

Iran ta harba jirage marasa matuƙa 300 da makamai masu linzami, kamar yadda ma’aikatar sojin Isra’ila ta tabbatar a ranar Lahadi.

Harin ya ƙunshi jirage marasa matuƙi 170 da makamai masu linzami 30 amma babu ɗaya daga cikin su da ya shiga cikin Isra’ila, sai kuma miyagun makamai masu linzami 110 waɗanda ƙalilan daga cikin su suka faɗa cikin Isra’ila, in ji mai magana da yawun dakarun Isra’ila Admiral Daniel Hagari a cikin wata sanarwa ta talabijin.

BBC ba ta iya tantance sashihancin alƙaluman ba.

Tazara mafi kusa a tsakanin Iran da Isra’ila ita ce kilomita 1,000 (Mil 620) ta ɓangaren Iraq da Syria da Jordan.

Harbo makamai daga ƙasashe daban-daban

A ranar Asabar Dakarun juyin-juya-hali na Iran suka ce sun ƙaddamar da hare-haren jirage marasa matuƙa da na makamai masu linzami.

Dakarun tsaron Iraqi sun shaida wa kafar yaɗa labaru ta Reuters cewa sun ga makamai na ratsawa ta sararin samaniyar ƙasar zuwa ɓangaren Isra'ila.

Iran ta ce bayan kimanin sa'a ɗaya an harba makamai masu linzami masu gudu ta yadda za su isa inda aka tura su kusana a lokaci guda.

Sashen tsaron Amurka ya ce ya kakkaɓo gwamman makamai masu linzami da jirage marasa matuƙa waɗanda aka harba daga ƙasashen Iran da Iraqi da Syria da Yemen.

Ita ma ƙungiyar Hezbollah mai samun goyon bayan Iran wadda ke a Lebanon ta ce ta harba wasu gungun makamai kashi biyu zuwa wani sansanin sojin Isra'ila da ke yankin tuddan Golan inda Isra'ila ta kankane, wani tudu da Isra'ila ta ƙwace daga hannun Syria lamarin da ƙasashen duniya da dama ke adawa da shi.

Isra'ila da ƙawayenta sun kakkaɓo akasarin makaman da Iran ta harba

Rear Admiral Hagari ya ce kimanin kashi 99 cikin 100 na makaman da Iran ta harba an kaɓo su ko dai gabanin su isa Isra’ila ko kuma a cikin sararin samaniyar ƙasar ta Isra’ila.

Makaman sun haɗa da dukkanin jirage marasa matuƙa da kuma makamai masu linzami waɗanda ke tafiya samɓal da kuma miyagun makamai masu linzami masu yin lauje.

Shugaban Amurka Joe Biden ya ce dakarun Amurka “sun taimaka wa Isra’ila wajen kakkaɓo kusan dukkanin” jirage marasa matuƙa da makamai masu linzami waɗanda Iran ta harba a ranar Lahadi.

A wata sanar, shugaban ya ce Amurka ta tura da jiragen yaƙinta na ruwa da na sama zuwa yankin gabanin harin.

...

Dakarun Amurka waɗanda ke aiki daga sansanonin da ba a bayyana ba a yankin sun kakkaɓo jirage marasa matuƙa da dama a sararin samaniyar kudancin Syria kusa da kan iyaka da Jordan, kamar yadda majiyoyin tsaro suka shaida wa kafar yaɗa labaru ta Reuters.

Shi ma Firaiministan Birtaniya Rishi Sunak ya tabbatar da cewa jiragen yaƙin saman Birtaniya na RAF Typhoon sun kakkaɓo jiragen sama marasa matuƙa na Iran.

Mista Sunak ya ce harin na Iran abu ne “mai haɗari wanda ke iya tayar da hankula kuma na yi Allawadai da shi.”

Jordan – wadda ke da yarjejeniya da Isra’ila kan amfani da sararin samaniyarta, amma kuma ta ke sukar Isra’ila kan matakin da take ɗauka a Gaza- ita ma ta ce ta kakkaɓo wasu makamai da suka ratso ta sararin samaniyarta domin kare al’ummarta, in ji wata sanarwa ta gwamnatin ƙasar.

Faransa ma ta taimaka wajen yin sintirin sararin samaniyar ta Isra’ila, sai dai bau tabbas ko ta samu nasara kaɓo wani makami, in ji sojin Isra’ila.

Makamai nawa ne suka faɗa Isra'ila kuma wace ɓarna suka yi?

A birnin Jerusalem, wakilin BBC ya bayyana cewa ya ji ƙarar jiniya tare kuma da ganin yadda shingen kariya na Isra’ila da ake kira Iron Dome ya riƙa aiki, wanda yake amfani da na’urar kula da zirga-zirga domin gano makaman roka, tare da tantance waɗanda za su iya faɗawa inda mutane suke da kuma waɗanda ba za su fada inda mutane suke ba.

Ana harba makaman kaɓo rokoki ne kawai a kan rokokin da ake tunanin za su faɗa a yankin da al’umma suke.

Rear Admiral Hagari ya ce ƙalilan daga cikin miyagun makamai masu linzamin ne suka faɗa cikin Isra’ila.

Ɗaya daga cikin su ya samu ‘wani ɓangare’ na sansanin sojin sama na Nevatim da ke cikin hamadar Negev a kudancin Isra’ila.

Hagari ya ce sansanin na ci gaba da aiki.

...

Sai dai kamfanin dillancin labaru na Iran IRNA, ya ce harin ya yi ‘mummunar illa’ ga sansanin sojin saman.

Amma Rear Admiral Hagari ya ce a jimilla mutum 12 ne suka jikkata a sanadiyyar harin.

Cikin su akwai wata yarinya mai shekara 12 daga al’ummar Larabawa mazauna kusa da birnin Arad, wadda aka ce wani tarkacen makamin da aka tarwatsa a sama a faɗo ya ji mata ciwo kuma an kwantar da ita a sashen masu neman kulawa ta musamman a asibiti.

Jordan ma ta ce wasu tarkacen sun faɗa a cikin ƙasarta sai dai ba su ji wa kowa rauni ba.

Me zai faru yanzu?

Kafar yaɗa labaru ta Channel 12 TV da ke Isra’ila ta ruwaito wani jami’in da ba a bayyana sunansa ba na cewa “za a mayar da martani” game da harin.

Yanzu haka Isra’ila da sauran ƙasashe masu maƙwaftaka sun sake buɗe sararin samaniyarsu, sai dai ministan tsaro na Isra’ila Yoav Gallant ya ce wannan takun-saƙa da Iran “ba ta ƙare ba”.

Sai dai a ɓangare ɗaya Iran ta gargaɗi Isra’ila cewa wannan hari “somin-taɓi ne kan wanda za ta ƙddamar matuƙar Isra’ila ta ce za ta mayar da martani”, kamar yadda shugaban ma’aikata na rundunar tsaron Iran Mano Janar Mohammad ya shaida wa kafar talabijin ta ƙasar.

Ya kuma ce za a kai hari kan sansanonin sojin Amurka matuƙar Amurkar ta ce za ta shigar wa Isra’ila.

Kwamandan dakarun juyin-juya-halin Iran, Hosse Salami ya ce Iran za ta mayar da martani a kan duk wani hari da Isra’ila ta kai kan wani abu mallakin Iran ɗin, ko jami’anta ko kuma ƴan ƙasarta.

Kwamitin tsaro na Majlisar ɗinkin duniya na shirin yin wata ganawa kan lamarin, kamar yadda Isra’ila ta buƙata.

Shi kuma shugaban Amurka, Joe Biden ya ce zai kira taron manyan ƙasashen duniya na G7 a ranar Lahadi domin duba yadda za a haɗa hannu a warware matsalar ta hanyar diflomasiyya.

Ire-iren makaman Iran masu linzami
People are also reading