Home Back

Wasu sun killace Tinubu sun tattare ko ina, bai san ‘yan Najeriya na fama da bakin yaunwa ba har yanzu – Ali Ndume

premiumtimesng.com 2024/8/21
Ba zan roki Saraki ba – Inji Ali Ndume
Ali Ndume

Sanata Ali Ndume na jam’iyyar APC, ya bayyana cewa akwai wadanda suka yi bababkere suka tattare ko’ina shugaban Tinubu bai san cewa ‘yan Najeriya na fama da tsananin bakin yunwa ba.

” Ina tabbatar muku ku sani cewa shugaba Tinubu baa su i san halin da ake ciki a kasar nan ba. Wasu sun tattare ko ina bai iya hangen abinda ke faruwa da talawa ‘yan Najeriya ba.

“’Yan Najeriya na kara fusata matuka, gwamnati ba ta yin komai kan karancin abinci, don haka akwai bukatar ta yi wani abu cikin gaggawa, ba mu da wurin ajiye abinci.

“Akwai karancin abinci, matsalar abinci ita ce mafi muni da kowace al’umma za ta iya fuskanta, idan muka kara da cewa matsalar tsaro za ta yi tsanani kuma” inji shi.

Ya dai kamat shugaba tinubu ya farka da barcin da yake ciki ya mike tsaye ya san abinda zai yi wa yan Najeriya cikin gaggawa,, domin a halinda ake ciki, wasu sun yi babakere sun tattare ko ina ya ya iya ganin gaban sa ballantana bayansa.

” Lallai ya kamata Tinubu ya bude kofarsa masu bashi shawara ta gari su garzayo su bashi, Domin abin akwai tsoro cikin sa, ba ma ga Tinubun ba har ni kai na abin zai iya shafata domin yana bani tsoro.

People are also reading